Mun fara ginin sabon gidan yari mai daukan mutum 3000 a Abuja, Gwamnatin tarayya

Mun fara ginin sabon gidan yari mai daukan mutum 3000 a Abuja, Gwamnatin tarayya

- Kwantrolan hukumar gidajen gyara hali ya kawo karshen zamaninsa

- Jami'an hukumar sun shirya masa fareti na musamman

- Ministan harkokin cikin gida ya jinjina masa bisa kokarin da yayi

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a ranar Alhamis ya bayyana cewa kawo yanzu gwamnatin tarayya ta saki fursunoni 4000 domin rage cinkoson gidajen yari a Najeriya.

Ministan ya kara cewa yana matukar farin ciki babu fursuna ko guda da ya kamu da cutar Korona a gidajen gyara halin kasar nan.

Aregbesola ya bayyana hakan ne a faretin karamci ga Kwantrolan hukumar gidajen gyara hali, Alhaji Ja'afaru Ahmed, yayinda yake shirin ritaya.

Ministan ya jinjinawa kwantrolan bisa kokarinsa da jajircewarsa wajen aiki.

Ya ce za'a tuna da shi bisa gina gidan yari mai iya daukan mutane 3000 a Janguza, jihar Kano.

Aregbesola ya bayyana cewa an kaddamar da gina wani sabon gidan yari a Karshi Abuja da kuma Bori a jihar Ribas.

DUBA NAN: 'Yan damfara da sunan COVID-19 sun bayyana a birnin Abuja, FCTA

Mun fara ginin sabon gidan yari mai daukan mutum 3000 a Abuja, Gwamnatin tarayya
Mun fara ginin sabon gidan yari mai daukan mutum 3000 a Abuja, Gwamnatin tarayya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jami'an Sojojin Najeriya dake faggen fama 127 sun ajiye aiki

Ministan ya ce karkashin kwantrolan, yanzu Fursunoni "23 na digir-gir, daya PhD; Masters 16 da kuma PGD 6."

"Jimillan Fursunoni 465 na karatun digiri irinsu zaman lafiya da sulhu; ilimin ta'addanci da tsaro, siyasa, da doka."

"Bugu da kari, 1,404 na rubuta SSCE da kuma 634 suka ci Credit 5... yayinda 4,757 suna karatun manya kuma 1,162 sun kammala."

A bangare guda, kotun daukaka kara dake zamanta a jihar Kano ta yi watsi da hukuncin daurin shekaru 10 da akayi wa Umar Farouq, matashin da ake zargi da kalaman batanci ga Annabi.

Bayan haka, kotun ta sake watsi da hukuncin da aka yiwa mawaki, Yahaya Aminu Sharif, inda ta ce a sake shari'ar daga farko, cewar rahoton BBC.

Shi ma Yahaya Aminu Sharrif ana zarginsa da kalaman batanci kan Annabi (SAW).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng