INEC: Yakubu zai mika ragamar mulki ga mukaddashin shugaba a ranar Litinin

INEC: Yakubu zai mika ragamar mulki ga mukaddashin shugaba a ranar Litinin

- Shugaban INEC mai sauka, Farfesa Mahmood Yakubu zai mika ragamar ma'aikatarsa ga mai rikon kwarya

- Dama wa'adin mulkin Farfesa Mahmoud zai kare ne a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, kafin a sabunta masa nadi

- Sakataren yada labaran INEC, Rotimi Lawrence Onyekanmi, ya sanar da hakan, inda yace sai majalisar tarayya ta amince tukunna

Shugaban INEC mai sauka, Farfesa Mahmood Yakubu zai mika ragamar ma'aikatar ga wani baturen zabe da zai yi rikon kwarya, har sai majalisar tarayya ta tabbatar da kara nadinsa a matsayin shugaban INEC din ko kuma akasin hakan.

Bayan shugaba Muhammadu Buhari ya kara zabar Yakubu, ya mika sunansa ga majalisar tarayya don tabbatar dashi, dama wa'adin mulkinsa na farko zai kare ne a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Dalilin da yasa na zabi Yar'Adua a kan Falae a zaben 1993 - Obasanjo

Ana sa ran zai mika ragamar mulkin hukumar ga kwamishinonin da nasu wa'adin bai kare ba, Daily Trust ta wallafa.

INEC: Yakubu zai mika ragamar mulki ga mukaddashin shugaba a ranar Litinin
INEC: Yakubu zai mika ragamar mulki ga mukaddashin shugaba a ranar Litinin. Hoto daga ChannelsTv.com
Asali: UGC

Akwai wasu kwamishinoni 5 da suka yi wa'adi biyu don haka basu da damar kara wani wa'adin.

Sakataran yada labaran INEC, Rotimi Lawrence Oyekanmi, ya sanar da wannan labarin.

KU KARANTA: EndSARS: IGP ya zargi kafafen sada zumunta da assasa rikici

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shugaban ma'aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari, zai jagoranci manyan ma'aikatan gwamnati zuwa wurare daban-daban a cikin kasa a matsayin daya daga cikin ayyukan da matasa suka bukaci a yi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tattauna da shugabannin gargajiya a kan matsalolin da Najeriya take fama da su, daga Daily Nigerian.

Ya rokesu da su taimaki mulkinsa wurin kwantar da tarzoma musamman wacce matasa suka tayar, a sanar da matasa cewa ya ji kukansu kuma yanzu haka yana iyakar kokarinsa wurin ganin ya daidaita al'amura.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel