Atiku ga Biden: A inganta mana tsaro, a cire takunkumi, mu karfafa alakarmu

Atiku ga Biden: A inganta mana tsaro, a cire takunkumi, mu karfafa alakarmu

A wani jawabi da Alhaji Atiku Abubakar, ya yi a Facebook da Twitter, ya taya Joe Biden da Kamala Harris murnar rantsar da su da aka yi a kasar Amurka.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriyar ya yi amfani da wannan dama ya roki sabuwar gwamnatin Amurka ta Joe Biden abubuwa uku da ya ke nema.

Legit.ng ta tattaro wadannan bukatu na Atiku Abubakar a madadin al’ummar Najeriya:

1. Yaki da ‘yan ta’adda

Bangare na farko da Atiku Abubakar yake so Amurka ta taimaka wa Najeriya shi ne yakar ta’addanci a yankin Arewa maso gabas da Arewa maso yamma.

Atiku Abubakar ya ce Najeriya ta na cikin wani yanayi da ya ke barazana ga yankin Afrika.

KU KARANTA: Za mu dawo - Trump

2. Cire takunkumi

Wata bukata da Atiku Abubakar ya gabatar a ranar Alhamis ita ce sabuwar gwamnatin Joe Biden ta cire duk wani takunkumi na hana ‘Yan Najeriya shiga Amurka.

Atiku ya tuna wa Joe Biden da Kamala Haris wata magana da George Bernard Shaw ya taba yi, inda ya ce Najeriya da Amurka kasa daya ce da harshe ya raba su.

3. Karfafa alakar da ke tsakani

Alhaji Atiku Abubakar, ya roki gwamnatin Biden ta karfafa dangantakar da ke tsakanin Amurka da Najeriya kamar yadda aka san kasashen biyun tun zamanin da.

KU KARANTA: 'Ya 'yan Trump sun gaza rika hawaye yayin da Mahaifinsu yake jawabin karshe

Atiku ga Biden: A inganta mana tsaro, a cire takunkumi, mu karfafa alakarmu
Atiku da Biden Hoto: businessday.ng/politics
Asali: UGC

A cewar Atiku, alakar Najeriya da kasar Amurka ta fara ne bayan ziyarar da Alhaji Tafawa Balewa ya kai wa takwaransa, John F Kennedy a shekarar 1961.

Wazirin Adamawa ya karasa jawabin na sa da cewa: “Har ila yau, ina taya ka murna, Ubangiji ya albakarkaci kasashenmu biyu, kuma ya sa wa’adinka ya yi kyau.”

Dazu kun samu labari cewa tuni har Joe Biden ya sa hannu a wasu dokoki 17, jim kadan bayan shiga ofishin shugaban kasa a ranar Laraba, 20 ga watan Junairu.

Joe Biden ya maida kasar Amurka cikin kungiyar WHO da yarjejeniyar 'Paris Climate Accord', sannan ya bada umarni a dakatar da batun gina katangar Mexico.

Da wannan dokoki da aka kawo, an ajiye maganar hana wasu kasashe shigowa cikin Amurka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel