Watakila NIN ya shiga sharudan rajistar katin zabe inji wani Ma'aikacin INEC

Watakila NIN ya shiga sharudan rajistar katin zabe inji wani Ma'aikacin INEC

- Babu mamaki INEC ta rika karbar NIN wajen yin rajista na CVR a Najeriya

- Wani babban Jami’in hukumar zabe ya ce sun fara kawo wannan maganar

- Amma kawo yanzu INEC ba ta cinma matsayar karshe a game da batun ba

Hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya, ta na la’akari da fara karbar NIN a matsayin sharadin rajistar masu shirin kada kuri’a a zabe.

Jaridar Punch ta rahoto cewa hukumar mai zaman kanta, na iya bukatar NIN daga wurin masu rajista da zarar an dawo da yin katin zabe na kasa.

Wani kwamishinan INEC na kasa ne ya fara kyankyasa wannan magana a lokacin da ya yi hira da jaridar a ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.

Jami’in hukumar zaben yake cewa NIN zai taimaka wajen magance matsalolin da ake samu a zabe.

KU KARANTA: Pantami ya yi magana game da shirin katin 'dan kasa

Ana ganin cewa karbar NIN za ta hana kananan yara da ba su kai shekara 18 ba yin zabe, sannan za a haramtawa sojojin gona kada kuri’a a Najeriya.

Bayan haka wannan jami’i ya ce bukatar NIN kafin ayi wa mutum rajistar katin zabe, zai dakile wasu matsalolin da ake fuskanta wajen rajistar jama'a.

Wannan babban jami’i bai bari a bayyana sunansa ba, domin kuwa ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu ba a gama cin ma matsaya kan batun ba.

Ya ce: “NIN shi ne ya dace. Idan za mu cigaba da rajistar katin zabe, za mu iya la’akari da aiki da shi, domin katin ‘dan kasa ake amfani da shi wurin zabe.”

KU KARANTA: NIMC ta kirkiro manhajar katin dan kasa a kan wayoyin hannu

Watakila NIN ya shiga sharudan rajistar katin zabe inji wani Ma'aikacin INEC
Katin zabe da na NIN Hoto: Shafin INEC da NIMC
Asali: UGC

“Ina iya fada maku cewa NIN zai zama cikin sharudan rajista idan an dawo CVR.” Inji kwamishinan.

Tun shekaru uku da su ka wuce hukumar gudanar da yin rajistar katin 'dan kasa (NIMC) ta bada sanarwar cewa, ta yi wa mutum fiye da miliyan 20 rajista.

Aadadin mutanen da hukumar NIMC ta yiwa rajista a watan Nuwamba na shekarar 2015 ba su zarce miliyan 7 ba. Zuwa yanzu, adadin ya karu matukar gaske.

Gwamnatin tarayya ta bada wa'adin rajistar layin waya da NIN a kokarinta na tattara bayanan 'yan kasa a wuri guda domin samun saukin matsalar tsaro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng