NDDC: Ban ba Abubakar Malami cin hancin Dala Miliyan 5 ba inji Akpabio

NDDC: Ban ba Abubakar Malami cin hancin Dala Miliyan 5 ba inji Akpabio

- Godswill Akpabio ya musanya jitar-jitar cewa ya ba Minista cin hanci

- Ana zargin Ministan da bada kudi domin a amince da nadinsa a NDDC

- Wasu na cewa nadin shugaban rikon kwarya a NDDC ya saba wa doka

Ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio, ya karyata zargin da ake yi masa na ba takwaransa, Abubakar Malami da wasu cin hanci.

Ana zargin Sanata Godswill Akpabio da ba Abubakar Malami SAN da kuma wasu kudi domin ya samu ya nada shugaban rikon kwarya a hukumar NDDC.

Tun da aka nada shugaban wucin-gadi a NDDC, ake zargin Ministan da yin karfa-karfa a hukumar.

Jaridar Premium Times ta ce ana zargin Godswill Akpabio da saba tsarin kama-kama da ake kai wajen rikon ma’aikatar mai kula da cigaban yankin Neja-Delta.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta ce a bude makarantu, Gwamna ya ce sam ba haka ba

Mai girma Ministan ya fito ya musanya zargin da ke kansa na cewa ya biya babban lauyan gwamnati watau AGF da wasu jami'ai kudi domin a biya masa bukata.

Jawabin Ministan ya fito ne ta bakin hadiminsa, Anietie Ekong, a ranar Asabar, 16 ga watan Junairu, 2021.

Jawabin ya ce:

“Hankalin Mai girma Ministan Neja-Delta, Sanata Godswill Akpabio, ya zo ga labarin bogi da ake yada wa na cewa ya ba Ministan shari’a, Abubakar Malami da wasu cin hanci da nufin a amince da shugaban rikon kwarya a NDDC.”

NDDC: Ban ba Abubakar Malami cin hancin Dala Miliyan 5 ba inji Akpabio
Sanata Godswill Akpabio Hoto: Premium Times www.premiumtimesng.com
Source: UGC

KU KARANTA: 2023: Kusoshin APC a kasar Yarbawa sun ce ba su san maganar Tinubu ba

“Wannan yunkuri ne da wasu bata-gari su ke yi domin bata sunan Mai girma Ministan Neja-Delta da Ministan shari’a, AGF. Wannan zargi ba gaskiya ba ne, sannan abin ban dariya ne."

Akpabio ya yi barazanar zuwa kotu a kan wannan zargi, ya ce wadanda ba su goyon bayan binciken kudin da ake yi a NDDC ne suka kitsa wannan jita-jita.

Kun samu labari cewa wata kungiya mai kare hakkin Jama'a ta sha alwashi za ta sa kafar wando daya da gwamnatin Buhari Buhari kan cin bashi da saida kadarori.

Kungiyar SERAP ta rubuta takarda ta na cewa ka da majalisar wakilai da dattawa su sake su kyale gwamnatin tarayya ta saida kadarorin da Najeriya ta mallaka.

SERAP tayi barazana cewa idan har ‘Yan majalisa ba suyi wani abu ba, za ta kai gwamnati kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel