Trump ya yi kwanan karshe a White House, Biden zai karbi ragamar Amurka

Trump ya yi kwanan karshe a White House, Biden zai karbi ragamar Amurka

- Yau Donald Trump zai bar mulkin kasar Amurka ba don yana so ba

- Za a rantsar da Joe Biden a matsayin sabon Shugaban kasar Amurka

- Trump zai yi wa wasu mutane afuwa kafin ya sauka daga kan kujera

Shugaban kasar Amurka mai barin-gado, Donald Trump, ya yi kwanansa na karshe a fadar White House a ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.

Jaridar Punch tace mako guda kenan aka shafe ba tare da an ga Donald Trump a fili ba, tun da aka dakatar da shugaban kasar daga Twitter, ya yi tsit.

Haka zalika har yanzu Trump bai taya Joe Biden murnar lashe zaben da aka yi ba, ko ya gayyace shi zuwa fadar shugaban kasa ko ya masa barka.

Daga cikin ayyukan da shugaban mai barin-gado zai yi karshe shi ne, zai ziyarci garin Florida a yau Laraba, inda zai yi wa wasu masu laifi afuwa.

KU KARANTA: Mun bar tarihi a Amurka - Gwamnatin Trump

Zuwa yanzu ba a san ko su wanene za ayi wa afuwar ba, amma da wahala shugaban ya sa kansa ko iyalinsa cikin jerin wanda za su samu wannan lamuni.

A gefe guda kuma Joe Biden wanda za a rantsar a matsayin sabon shugaban kasa, ya bar mazaunarsa ta Deleware, ya iso birnin Washington DC.

Bayan Biden da iyalinsa, ita ma mataimakiyar shugaban kasa mai jiran-gado, Kamala Harris ta iso Washington bayan ta sauka daga kujerarta na Sanata.

Da kimanin karfe 12:00 na ranar yau ne za a rantsar da Joe Biden a kan kujerar shugaban kasa.

KU KARANTA: Mathew Kukah ya samu shiga wurin Fafaroma, ya zama Mai bada shawara

Trump ya yi kwanan karshe a White House, Biden zai karbi ragamar Amurka
Shugaba Trump zai bar ofis Hoto; Getty Images
Asali: Getty Images

Rahotanni sun tabbatar da cewa an baza dakaru a babban birnin domin tabbatar da tsaro. Sannan kuma ana bada tazara wajen zama saboda annobar COVID-19.

A baya kun samu labari cewa Joe Biden zai yi karin kumallo ne da dokar da gwamnatin Donald Trump da zai gada ta ya kakabawa wasu kasashen Musulmai.

Tun a yau ne Joe Biden zai cire dokar da ta hana mutanen wasu kasashe shigowa Amurka.

Wata takarda da ta fara yawo a ranar Asabar ta nuna cewa dokar da Donald Trump ya kakaba wa wadannan kasashe ba za ta kwana a gwamnatin Joe Biden ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng