Kwantan ɓauna: Yan bindiga sun kashe jami'an sa-kai 7 a Niger

Kwantan ɓauna: Yan bindiga sun kashe jami'an sa-kai 7 a Niger

- Yan bindiga sun kashe jami'an sa-kai bakwai a karamar hukumar Mashegu da ke jihar Niger

- Maharan sun kuma raunata wasu da dama tare da kona baburansu fiye da 50

- Hakan na zuwa ne bayan hukumomin tsaro sun kona wani sansanin yan bindiga a jihar

Yan bindiga a ranar Litinin sun kashe yan-sa-kai bakwai a wani harin bazata da suka kai karamar hukumar Mashegu na jihar Niger sannan suka kona fiye da Babura 50 mallakar yan dokan.

Harin bazatan na zuwa ne yayinda yan bindigan da aka tura yankin suka kaddamar da wani hari a mabuyar yan bindigan da ake zaton sun kashe manoma bakwai a yankin a makonni biyu da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: A daina yi wa makiyaya kudin goro, suna da yancin zama a duk inda suke so, Shehu Sani ga Akeredolu

Kwantan ɓauna: Yan bindiga sun kashe jami'an sa-kai 7 a Niger
Kwantan ɓauna: Yan bindiga sun kashe jami'an sa-kai 7 a Niger Hoto: @GuardianNigeria
Source: Twitter

Majiyoyi sun ce wani bara-gurbi a cikin yan-sa-kan ne ya fesa harin da aka kai, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yan bindigan sun mamaye yan tsaron sa-kan ne a yayinda suke kawo karshen harinsu.

“Yan bindigan sun bude wuta kan yan-sa-kan inda suka kashe bakwai daga cikinsu a nan take sannan suka raunata wasu da dama. Yan bindigan sun kuma cinnawa fiye da babura 50 wuta na jami’an tsaron wanda aka ajiye dan tazara kadan daga inda suke gudanar da taronsu,” in ji majiyar.

A halin da ake ciki, babban sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Ahmed Matane, wanda ya tabbatar da ci gaban ya bayyana abun a matsayin “abun bakin ciki sosai.”

KU KARANTA KUMA: Kamar Trump, ba za a manta da Shugaba Buhari ba, In ji Fayose

“Kwanan nan hukumomin tsaro suka kona wani sansanin yan bindigan,” in ji shi.

A wani labarin, rundunar 'yan sandan Najeriya ta damke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka addabi jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Daily Trust ta wallafa.

An kama daya daga cikin ma'aikatan tsaro na jami'ar mai suna Aliyu Abubakar sakamakon bai wa masu garkuwa da mutanen tallafi a dukkan lokutan da suke sace jama'a a jami'ar.

Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, CP Frank Mba, ya sanar da damke wani Malam Jafaru da ke samar da asiri ga masu garkuwa da mutanen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel