Kamar Trump, ba za a manta da Shugaba Buhari ba, In ji Fayose

Kamar Trump, ba za a manta da Shugaba Buhari ba, In ji Fayose

- Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya aika gagarumin sako ga Shugaba Buhari

- Fayose ya bukaci Shugaban kasar da ya tabbatar da ganin an tuna dashi na akhairi bayan ya bar mulki a 2023

- A cewarsa, rashin tsaro ya zama ruwan dare a Najeriya a karkashin gwamnatin APC

Yayinda Donald Trump ya sauka daga matsayin Shugaban kasar Amurka, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ba shugaan kasa Muhammadu Buhari wata shawara.

Legit.ng ta rahoto cewaa Fayose a cikin wasu jerin wallafa da yayi a shafin Twitter a ranar Talata, 19 ga watan Janairu, ya yi zargin cewa abubuwa sun kara tabarbarewa cikin shekaru biyar da suka gabata na gwamnatin Buhari.

Ya ce tattalin arziki da tsaron kasar sun durkushe, inda ya kara da cewa an lalata zabuka na gaskiya da hadin kan kasar.

Kamar Trump, ba za a manta da Shugaba Buhari ba, In ji Fayose
Kamar Trump, ba za a manta da Shugaba Buhari ba, In ji Fayose Hoto: @GovAyoFayose
Asali: Twitter

Ya wallafa a Twitter:

“Duk wani abu mai amfani an lalata shi a karkashin kulawar Buhari. Duk wani abu mai muhimmanci da muke dashi a matsayin kasa- tattalin arziki, tsaro, yancin dan adam, doka, zabbuka na gaskiya da hadin kan kasar duk an lalata su.”

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Talakawan Nigeria miliyan 24 za su dunga karban N5,000 kowannensu na tsawon watanni 6, in ji FG

Tsohon gwamnan ya kara da cewa yan Najeriya ba za su taba mantawa da shugaba Buhari ba bayan ya bar kujerar mulki a 2023 kan tarin lalacewar da kasar tayi.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta shirya tallafawa yara 10m da ba sa makaranta

A wani labari na daban, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya jadadda cewa yayi wuri da za a fara tattauna yadda zaben 2023 zai kasance.

A cewar jaridar The Nation, tsohon Shugaban kasar yak an bayar da irin wannan amsar a duk lokaccin da aka tambaye shi ko yana da wani shiri da yake na takarar zaben Shugaban kasa na gaba.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa kyakkyawar alakar da ke bunkasa a tsakanin Jonathan da wasu shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na haddasa fargaba a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel