A daina yi wa makiyaya kudin goro, suna da yancin zama a duk inda suke so, Shehu Sani ga Akeredolu

A daina yi wa makiyaya kudin goro, suna da yancin zama a duk inda suke so, Shehu Sani ga Akeredolu

- Shehu Sani ya yi Allah-wadai da korar makiyaya da gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya yi daga jiharsa

- Tsohon sanatan ya ce suma yan kasa ne kuma suna da yancin zama a duk inda suke muradi

- Sani ya ce laifin wani baya shafar wani don haka kamata yayi ayi maganin fitinannun ciki

Tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bukaci gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da ya sake tunani kan hukuncinsa da ke umurtan Fulani makiyaya su bar dazukan jihar.

Akeredolu ya bayar da umurnin a ranar Litinin a cikin wata sanarwa, biyo bayan hauhawan rashin tsaro a jihar duk da kaddamar da jami’ an tsaro na Amotekun da aka yi.

Ya umurci makiyaya da su bar dazukan jihar Ondo cikin kwanaki bakwai.

A daina yi wa makiyaya kudin goro, suna da yancin zama a duk inda suke so, Shehu Sani ga Akeredolu
A daina yi wa makiyaya kudin goro, suna da yancin zama a duk inda suke so, Shehu Sani ga Akeredolu Hoto: Senator Shehu Sani
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Kamar Trump, ba za a manta da Shugaba Buhari ba, In ji Fayose

Tsohon sanatan a wani dan gajeren sako zuwa ga gwamnan a shafinsa na Facebook ya ce ba daidai bane a bukaci dukkanin makiyaya su bar jihar yayinda suke da yancin zama a duk inda suke so a kasar.

Ya kara da cewa ya zama dole gwamnati a dukkan matakai ta yi kokarin hukunta wadanda suka saba doka sannan su mutunta yancin wadanda basu ji ba basu gani ba.

Ya ce:

“Ya kai Gwamnana Akeredolu, ina sane da matsalolin tsaron da jiharka ke fuskanta.

“Na yaba da kokarinka, amma ba daidai bane a nemi dukkanin makiyaya su bar dazukan Ondo.

“Kada laifin yan tsirarun miyagu ya shafi wadanda ke zama lafiya da bin doka wadanda ke da yancin yin rayuwa da yawo a duk yankunan kasarmu.

“Ya zama dole a ci gaba da yin duk wani kokari don maganin masu take doka, da kuma mutuntawa da kare yancin wadanda basu ji ba basu gani ba.”

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Talakawan Nigeria miliyan 24 za su dunga karban N5,000 kowannensu na tsawon watanni 6, in ji FG

A gefe guda, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta soki umarnin gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, na korar makiya daga dazukan Jihar Ondo.

Premium Times ta ruwaito umarnin Akeredolu a ranar Litinin, a wani mataki na dakile garkuwa da mutane a jihar.

Fadar shugaban kasar ta kuma bayyana bukatar da ke akwai na rashin danganta yanki, kabila ko addini da laifuka ko ta'addanci sai dai a ware laifin gefe guda a magance shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng