Ooni da Ataoja sun ba takarar tsohon Gwaman Legas, Bola Tinubu goyon-baya

Ooni da Ataoja sun ba takarar tsohon Gwaman Legas, Bola Tinubu goyon-baya

- Wasu ‘Yan siyasa suna ta kokarin tallata Bola Tinubu ga manyan Sarakuna

- Yanzu Jigon na APC ya samu karbuwa a wajen Sarakunan Ife da na Osogbo

- Sarakunan sun ce Tinubu ya cancanci ya yi takarar kujerar shugaban kasa

Yunkurin da wasu magoya-bayan magoyan jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu suke yin a saida shi a wajen sarakunan kasar Yarbawa ya fara kasuwa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu kwarin gwiwar takara bayan ya samu yabo da na’am daga wasu Sarakuna biyu.

Mai martaba Ooni na kasar Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi da kuma Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Olanipekun duk sun yabi tsohon gwamnan na jihar Legas.

A cewar wadannan manyan kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shirya karbar ragamar mulkin Najeriya.

KU KARANTA: Yankin Arewa zai dade a matsala, Dattawa sun soki mulkin APC

Sarki Oba Adeyeye Ogunwusi ya shaida wa magoya-baya cewa kishin-kishin din takarar Bola Tinubu alamun nasara ce ga kabilar Yarbawan kasar nan.

Sarkin ya kira ‘dan siyasar jinin Oduduwa, wanda ta tatsonsa ne aka samu Yarbawa. A cewar Oba, za a samu wasu ‘yan siyasar da za su yi wa Bola Tinubu adawa.

Oba Adeyeye Ogunwusi ya ce don haka magoya-baya da sauran Yarbawa za su cinma wannan buri ne idan suka hada-kai, suka yi amfani da hikimar siyasa.

Shi ma Oba Olanipekun ya jinjina wa Tinubu saboda yadda yake tallafa wa mutanen da ke zagaye da shi.

KU KARANTA: Rikicin Kwankwaso-Ganduje yana bata sunan Kano – Hadimin Gwamna

Ooni da Ataoja sun ba takarar tsohon Gwaman Legas, Bola Tinubu goyon-baya
Bola Tinubu Hoto: www.theyorubablog.com
Asali: UGC

Mai martaba Oba Olanipekun ya ce lokaci ya yi da tsohon gwamnan na Legas zai fito takara. “Asiwaju ya taimaka wa mutane. Lokaci ya yi da zai nemi takara.”

Ya ce: “Babu shakka ya cancanci ya yi takara. Ya na sauraron jama’a, wannan abu ne mai kyau.”

Sarakunan sun bayyana haka ne lokacin da ‘yan kungiyar South West Agenda, mai goyon-bayan Tinubu ya tsaya takarar shugaban kasa ta kai masu ziyara.

Sanata Dayo Adeyeye shi ne ya kai maganar takarar Bola Tinubu gaban Sarkin kasar Ife. Adeyeye ya ce Arewa na yunkurin raba-kan Yarbawa saboda siyasar 2023.

Tsohon Sanatan Ekiti, Dayo Adeyeye, ya yi kira ga Sarakunan su ja hankalin duk 'yan siyasan yankin Kudu da ke harin takara a 2023 su hakura, su kyale Tinubu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng