Arewa na bukatar shekaru fiye da 100 kafin a ga karshen matsalar tsaro inji Kungiya

Arewa na bukatar shekaru fiye da 100 kafin a ga karshen matsalar tsaro inji Kungiya

- Northern Elders for Peace and Development ta koka a kan matsalar tsaro

- Kungiyar Dattawan Arewan tace yankin na fuskantar rashin zaman lafiya

- Dattawan sun bukaci Buhari yayi kokarin kawo masu kwanciyar hankali

A ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021, wasu dattawan Arewacin Najeriya su ka fito su ka bayyana tsoronsu game da halin da ake ciki a yankin.

Jaridar Punch ta rahoto dattawan suna cewa ‘yan ta’addan Boko Haram, miyagun ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun yi wa Arewacin kasar zobe.

Dattawan yankin sun kuma yi barazanar zuga mutanen Najeriya da ke sauran bangarori su kaurace wa jam’iyyar APC mai mulki a zaben da za ayi a 2023.

Coalition of Northern Elders for Peace and Development ta bukaci a kawo sabbabin dabaru da za ayi amfani da su wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro.

KU KARANTA: Mathew Kukah ya samu shiga a Majalisar Fafaroma bayan an yi masa ca

Kungiyar ta Coalition of Northern Elders for Peace and Development ta ce za ta dauki mataki idan gwamnatin tarayya ta cigaba da watsi da kukan da ta ke yi.

Kamar yadda jawabin da shugaban da ke kula da wannan kungiya, Zana Goni, ya yi ya nuna, za a dauki shekaru sama da 100 ana fama da matsalolin yankin.

Jawabin Malam Zana Goni ya ce: “Ko da yaki ya tsaya a yau, daga abin da muke gani a kasa, zai dauki shekaru 100, Arewa maso gabas bai dawo daidai ba.”

“Manoma ba za su iya zuwa gona a yau, musamman a Arewa maso gabas, tsoronmu a shiga fama da yunwa idan ba a shawo kan lamarin ba.” Inji wannan kungiya.

KU KARANTA: COVID-19: Buhari ya yi alkawarin taimaka wa Imo - Uzodinma

Arewa na bukatar shekaru fiye da 100 kafin a ga karshen matsalar tsaro inji Kungiya
Shugabannin hafsun sojoji Hoto: Twitter Daga: @BashirAhmaad
Source: Twitter

Kungiyar ta ce Arewa ce kashin-bayan karfin APC. Ta ce idan babu zaman lafiya, “Babu yadda mu ka iya, dole mu zuga jama’a su guje wa APC idan 2023 ta zo.”

A halin yanzu da wannan kungiya ta ke wannan magana, jami'an tsaro suna ta samun galaba a kan 'yan ta'addan Boko Haram da 'yan bindigan da ke Arewa.

Kwanan nan Sojojin Najeriya na Operation Hadarin Daji su ka kashe wasu niyagun ‘yan bindiga sama da 30 yankunan Bungudu da Muradun a jihar Zamfara.

Kafin nan kuma dakarun na Operation Hadarin Daji sun fatattaki 'yan ta'adda akalla 50 a kauyen Kuriya da ke karamar hukumar Kaura Namoda, duk a Zamfara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel