Adeyeye ya ce Arewa na neman jawo sabani a Kudu maso yamma a kan zaben 2023

Adeyeye ya ce Arewa na neman jawo sabani a Kudu maso yamma a kan zaben 2023

- Dayo Adeyeye ya kai maganar takarar Bola Tinubu gaban Sarkin kasar Ife

- Sanata Dayo Adeyeye ya roki Mai martaba ya ba Jagoran APC goyon-baya

- Sarki ya ba masu goyon bayan Bola Tinubu shawarar abin da ya dace su yi

Tsohon Sanatan kudancin Ekiti, Dayo Adeyeye, ya yi kira ga Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi ya yi kira ga masu harin takara a 2023 duk su hakura.

Sanata Dayo Adeyeye ya na so a tursasa wa duk wani mai harin kujerar shugaban kasa a 2023, ya janye niyyarsa, ya kyale Asiwaju Bola Tinubu ya yi takara.

Jaridar Punch ta rahoto Dayo Adeyeye ya na mai wannan kira ne a lokacin da ya jagoranci wasu manyan ‘yan siyasar Yarbawa zuwa fadar Sarkin kasar Ife.

Tsohon mai magana da yawun bakin Sanatocin kasar ya shaidawa mai martaban cewa Asiwaju Bola Tinubu bai aika kowa ya fara yi masa yakin zabe ba.

KU KARANTA: PDP ta na farautar babban Jagoran APC, Okorocha gabanin 2023

A cewar Dayo Adeyeye, kungiyarsu ta SWAGA ta duba ta ga cewa babu ‘dan siyasar Yarbawa da zai iya samun nasara a zaben 2023, illa Bola Tinubu.

Ya ce: “Muna rokon Ooni da sauran Sarakuna, su tabbatar an samu hadin-kai a wajen takarar. Duk wanda za ayi wa magana, ayi, domin a fito da wanda ya dace.”

Sanata Dayo Adeyeye ya cigaba da cewa: “Wasu ‘yan siyasar Arewa suna so su yi amfani da mutanen Yarbawa, su raba kan yankin Kudu maso yamma.”

‘Dan siyasar ya ce Asiwaju zai iya kawo wa yankin kudu maso yamma kujerar shugaban kasa.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Gwamnan PDP ya ba Buhari shawara

Adeyeye ya ce Arewa na neman jawo sabani a Kudu maso yamma a kan zaben 2023
Sanata Dayo Adeyeye Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: UGC

A jawabinsa, Oba Adeyeye Ogunwusi ya yi kira ga masu goyon-bayan Tinubu su hada-kai, su yi amfani da hikima wajen cin ma manufarsu, su guji karfa-karfa.

Jiya kun ji cewa wasu tsofaffin shugabannin majalisun jihohin Ondo da Ekiti sun karyata rahoton da ke yawo na cewa su na goyon bayan Bola Tinubu ya yi takara.

‘Yan siyasar sun fito sun ce ba su yi alkawarin za su goyi bayan takarar Tinubu a zaben 2023 ba.

Wadannan ‘yan siyasa sun bayyana cewa sun halarci taron da Rt. Hon. Mudashiru Obasa ya kawo maganar, amma ba su tsaida cewa zasu goya wa Tinubu baya ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel