Magaji ya koka game da Sabanin Ganduje da Kwankwaso, "ya jawowa Kano rashin cigaba"
- Mu’azu Magaji ya cigaba da yin kira domin ‘Yan siyasar Kano su hada-kansu
- Dan Sarauniya ya ce wasu tsirarru ne su ka hada Kwankwaso da Ganduje fada
- Hadimin Gwamnan ya ce wadannan mutane ba su da abinci har sai an yi rikici
Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji, ya na takaicin rashin jituwar da ke tsakanin gwamna Abdullahi Ganduje da Rabiu Kwankwaso.
Jaridar Daily Trust ta rahoto Injiniya Mu’azu Magaji ya na cewa sabanin da ke tsakanin wadannan manyan ‘yan siyasar yayi tasiri a cigaban Kano da sunan jihar.
A cewarsa, hadin-kan gwamna da Rabiu Kwankwaso zai kawo zaman lafiya da cigaba a Kano, wanda hakan zai sa jihar ta koma rike da martabar da aka santa a Duniya.
Da yake wasu bayanai a shafinsa na Facebook kamar yadda ya saba, Injiniya Magaji ya zargi wasu ‘yan siyasa da hada Ganduje da bangaren ‘Yan Kwankwasiyya fada.
KU KARANTA: Abba Kyari: Kwamishanan da Ganduje ya sallama ya kamu da Coronavirus
Hadimin gwamnan ya ce wasu (bai ambaci suna ba) sun hada wannan rigima ne saboda son-kansu.
Dan Sarauniya ya ce idan ‘yan siyasar suka ajiye bambancinsu a gefe guda, jihar za ta amfana sosai, kamar yadda a baya aka yi wa Kanawa aikin da kowa ya amfana.
Tsohon Kwamishinan ya yi rubutu: “Sai yanzu na ke fahimtar menene dalilin da yasa jahilan nan ba su son sulhu a Kano. Su idan dai babu fitina a kullum to basu da gurbin zama, tun da ba kwarewa ce ko ilimi ya kawo su ba, sai dai gulma, munafinci, hada fitina, sukar mutane da hana alheri a ofishin gwamnati, tare da banbadancin banza da wofi a ofishin siyasa.”
KU KARANTA: Ina tare da Ganduje har gobe - Dan Sarauniya
A ranar Talatar, ya sake cewa: “Sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje rufin asiri ne da karin martaba ga su biyun. Kuma karin mutunci da martabar jihar Kano zai haifar”
A baya Magaji ya rubuta: “Wasu shaidanu da basu son ayi sulhu, sai bankado bayanan baya na Ganduje su ke yi a kan Kwankwasiyya….sai kuma ga wasu bayanan masu ratsa jiki kan alheri da akidar tafiyar da aka yi tare kan talaka da Kano.”
Ya cigaba da cewa: “A karshe dai, da ace ba a mantawa da baya to da a duniya ma ba za a daina yake-yaken kashe juna ba, ballan-tana adawar banbancin ra'ayi a siyasa.”
Idan za ku tuna, Mu’azu Magaji shi ne shugaban aikin NNPC-AKK da ake yi a Kano yanzu.
Bayan watanni 6 da rasa kujerar kwamishinan ayyuka, gwamna Abdullahi Ganduje ya dawo da Muazu Magaji cikin gwamnatinsa, ya ba shi wannan kujera.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng