'Yan Najeriya miliyan 21 su na da rajista ta dan ƙasa - NIMC

'Yan Najeriya miliyan 21 su na da rajista ta dan ƙasa - NIMC

Hukumar gudanarwa da yin rajistar dan kasa (National Identity Management Commission (NIMC) ta bayar da sanarwar cewa, a yanzu akwai kimanin 'yan Najeriya miliyan 21.4 da ta yi wa rajista ta dan kasa da kuma bayar da lambobi tantancewa

A ranar Litinin din da ta gabata, shugaban hukumar ta NIMC Aliyu Aziz, ya bayar da sanarwar hakan yayin ganawa da manema labarai na NAN (News Agency of Nigeria) a babban birnin tarayya.

Mista Aziz ya ce an samu sabon adadin wadanda hukumar ta yiwa rajista bayan an ƙare aikin ranar 6 ga watan Satumba, kuma a yanzu haka akwai cibiyoyi 805 da hukumar ta kafa a yankuna daban-daban cikin jihohi 36 a fadin kasar nan.

'Yan Najeriya miliyan 21 su na da rajista ta dan kasa - NIMC
'Yan Najeriya miliyan 21 su na da rajista ta dan kasa - NIMC

Yake cewa wannan mataki da hukumar ta kai, ya dace da manufarsu ta yiwa 'yan Najeriya miliyan 28 rajista kafin watan Dasumba na karshen shekarar nan.

KU KARANTA: Wasu mata 2 'yan kunar bakin wake sun tayar da bam a jihar Borno

Shugaban hukumar ya cigaba da bayani cewa, duba da irin kalubale da hukumar take fuskanta, domin da yawan 'yan Najeriya sun ki fita a yi musu rajista sanadiyar rashin son bin layi wanda a cewar sa idan sun yi hakuri na 'yan lokuta ne kadan.

Ya ke tunatarwa kuma, adadin da hukumar ta yiwa rajista a watan Nuwamba na shekarar 2015 ba su wuci miliyan 7 ba a yayin da ya karbi shugabancin hukumar.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel