Katin zama dan kasa: Duk laifin yan Najeriya, mu canza halin mu, Minista Pantami

Katin zama dan kasa: Duk laifin yan Najeriya, mu canza halin mu, Minista Pantami

- Dakta Isa Ibrahim Pantami ya yi kira ga yan Najeriya su gyara dabi'unsu

- Ministan ya ce matsalolin da ake samu wajen rijistan NIN ba laifin hukumar bane

- Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya ta ce ba za ta katse masu amfani da layin sadarwar ba

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dakta Isa Ali Pantami, ya daurawa yan Najeriya laifin saba dokokin COVID-19 yayinda suka je rijistan lamban katin zama dan kasa a fadin tarayya.

Yayin hirarsa da Channels TV ranar Juma'a, Pantami ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda yan Najeriya ke dandazo a ofishoshin hukumar rijistan katin zama dan kasa NIMC.

"Yan Najeriya za su je wajen, sunayensu ba sa cikin jerin wadanda za'a dauki bayanansu a ranar, amma zasu tsaya a wajen su ki wucewa, ko an fada musu su tafi ba zasu tafi ba. Ko jami'an tsaro sun rokesu su tafi ba zasu ji ba," yace.

"Dukkan wadanda kuke gani a Abuja ko Legas, kashi 90% zuwa 95% cikin ba su cikin wadanda aka gayyata don daukar hotonsu. Kawai suna zuwa wajen ne su na tsayawa."

"Wannan shine matsalan da muke fuskanta. Wannan ba matsalan hukuma bane. Wannan matsalan yan Najeriya ne. Ya kamata mu canza halayenmu."

Pantami ya ce ma'aikatarsa da NIMC na kokarin canza salon rijistan katin zama dan kasa da kuma hadawa da layukan waya.

Ya yi bayanin cewa ma'aikatarsa, NIMC da kamfanonin sadarwa za su sake duba lamarin idan gwamnatin tarayya ta kafa dokar kulle sakamakon waiwayen cutar Korona ta biyu.

KU KARANTA: Sai bayan awanni 3 da muka kira yan sanda suka zo, shugaban APC da aka sacewa yara 7

Katin zama dan kasa: Duk laifin yan Najeriya, mu canza halin mu, Minista Pantami
Katin zama dan kasa: Duk laifin yan Najeriya, mu canza halin mu, Minista Pantami Hoto: @FMoCDENigeria
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kwana 3 jere, sama da sabbin mutane 1500 suka kamu da Koronan kullum

A bangare guda, Legit ta ruwaito Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya ta ce ba za ta katse masu amfani da layin sadarwar ba sakamakon ci gaba da alakanta lambobin shedar kasa (NINs) da katinan SIM.

An ruwaito mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Adinde yana cewa wani binciken da aka gudanar kwanan nan akwai kusan katinan SIM guda hudu zuwa biyar ga kowane dan Najeriya mai amfani da waya.

Ya ce wannan ya bayyana dalilin bayar da damar hada layukan SIM har guda bakwai zuwa NIN guda daya ta musamman a cikin wata sabuwar hanyar da gwamnatin Najeriya ta bude kwanan nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng