NIMC ta kirkiro manhajar katin dan kasa a kan wayoyin hannu

NIMC ta kirkiro manhajar katin dan kasa a kan wayoyin hannu

- Hukumar NCC mai kula da harkokin kamfanonin sadarwa ta bukaci a hada kowacce lambar da lambar katin dan kasa

- Tun bayan fitowar sanarwar 'yan Nigeria ke tururuwa a ofisoshin hukumar NIMC domin bayar da lambobin wayoyinsu ko kuma mallakar katin dan kasa

- Domin saukaka hada lambar waya da lambobin NIN, NIMC ta kirkiri wata sabuwar manhaja domin saukaka al'amura

NIMC, hukumar da gwamnatin tarayya ta dorawa alhakin bayar da katin dan kasa, ta kirkiri sabuwar manhajar wayar hannu domin amfanin 'yan kasa, kamar yadda BBC ta rawaito.

Hukumar ta bukaci 'yan Nigeria su sauke manhajar a wayoyinsu na hannu domin samun saukin tafiya da shaidarsu ta zama 'yan kasa a cikin wayar salula koda yaushe, Kuma a duk inda suke.

A cikin watan Disambar na shekarar 2020 ne hukumar NCC ta bukaci kamfanonin sadarwa su hada lambobin wayar 'yan kasa da lambar tantancewa da NIMC ta bayar.

KARANTA: Fadar shugaban kasa ta radawa jam'iyyar PDP sabon suna na wulakanci

Za'a iya sauke sabuwar manhajar daga shagon manhajoji na Google Play ga masu amfani da wayoyin android.

NIMC ta kirkiro manhajar katin dan kasa a kan wayoyin hannu
NIMC ta kirkiro manhajar katin dan kasa a kan wayoyin hannu @BBC
Asali: Twitter

Kazalika, masu amfani da iPhone zasu iya samun manhajar a Apple Store.

Manhajar zata yi aiki ne a kan wayoyin 'yan kasa da suka mallaki lambobin NIN wadanda ke jikin katin shaidar zama dan kasa.

KARANTA: Sanata Shehu Sani: Abubuwa 10 da duk mai sha'awa ko burin shiga siyasa a Nigeria ya kamata ya sani

Bayan sauke manhajar tare da kaddamar da ita ta hanyar saka lambobin NIN, mutum zai iya hada lambarsa ta waya daga manhajar.

Akwai matakai da bayanai cikin sauki akan yadda za'a sarrafa manhajar da kuma amfani da ita akan waya ta yadda ba sai mutum yana yawo da katin shaidar dan kasa ba.

A wani labarin na Legit.ng Hausa, Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, ya ce babu gurbin tsarin kama-kama mulkin kasa a cikin kundin tsarin mulkin APC.

Tsohon gwamnan kuma sanatan Kano ta tsakiya ya ce cancanta ce ya kamata ta zama abar dubawa a zaben gaba.

Shekarau ya yi tsokaci akan alakar da ke tsakaninsa da gwaman Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da tsohon gwamna Kwankwaso.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel