Da duminsa: Bayan watanni 6 da saukeshi, Ganduje ya dawo da Muazu Magaji cikin gwamnatinsa

Da duminsa: Bayan watanni 6 da saukeshi, Ganduje ya dawo da Muazu Magaji cikin gwamnatinsa

- Gwamna Ganduje ya mayar da ma'aikatansa da ya sallama a baya bakin aiki

- Tun ba'a gama maganar Dawisu ba, labarin Muazu Magaji ya sake shigowa

- Tsohon kwamishanan ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook ta hanyar raba labarin Solacebase

Bayan kimanin watanni shida da sauke tsohon kwamishanan ayyukan jihar Kano, Muazu Magaji, kan murnar mutuwar marigayi Abba Kyari da yayi, an dawo da shi cikin gwamnati.

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya sake nadashi shugaban kwamitin ayyukan bututun mai da masana'antu.

Hakan na kunshe cikin jawabin da Uba Abdullahi, mai magana da yawun Sakataren gwamnatin jihar, ya saki, PremiumTimes ta samu.

LEGIT HAUSA ta ruwaito muku yadda Ganduje ya sallami Muazu Magaji bayan ya yi jawabi da aka fassara matsayin murnar mutuwan shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

Abba Kyari ya rasu a watan Afrilu bayan kamuwa da cutar Coronavirus kuma an yi jana'izarsa a birnin tarayya Abuja.

KU DUBA: Bidiyo da hotunan sabon sarkin Zazzau ya kai wa sarkin Kano, Aminu Bayero, ziyara

Da duminsa: Bayan watanni 6 da saukeshi, Ganduje ya dawo da Muazu Magaji cikin gwamnatinsa
Da duminsa: Bayan watanni 6 da saukeshi, Ganduje ya dawo da Muazu Magaji cikin gwamnatinsa Hoto: Muaz Magaji/Facebook
Asali: Facebook

Daga baya shima Allah ya jarabesa da kamuwa da cutar amma ya samu saukin bayan jinya a cibiyar killace masu cutar.

Tuni ya bada hakuri bisa furucin da yayi a lokacin kuma ya yi nadamar hakan.

Mayar da Muazu Magaji ya biyo bayan mayar da Salihu Tanko Yakassai, wanda aka fi sani da Dawisu, bakin aikinsa na babban hadiminsa na kafafen yada labarai.

DUBA NAN: Hanan Buhari da Mijinta Muhammad Turad sun saki hotunansu na farko bayan aure

Ganduje ya yi hakan ne makonni biyu bayan dakatad da shi daga mukaminsa kan sukan shugaba Muhammadu Buhari da yayi a shafinsa na Tuwita.

Dawisu ya ce ba'a taba gwamnati marasa tausayi irin ta shugaba Buhari ba.

Salihu Tanko Yakassai ya bayyana hakan da safiyar Juma'a a shafinsa na Tuwita inda ya mika godiyarsa ga jama'an da suka taya sa farin cikin komawa bakin aiki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel