Matthew Hassan Kukah zai rika ba Fafaroma shawara a kan kare hakkin Bil Adama

Matthew Hassan Kukah zai rika ba Fafaroma shawara a kan kare hakkin Bil Adama

- Kasar Vatican ta yaba da aikin da Bishof Matthew Hassan Kukah ya ke yi

- Limamin Katolikan ya samu wurin zama a majalisar Fafaroma zuwa 2026

- A kwanakin nan an yi ta sukar Faston saboda taba shugaban kasa Buhari

Birnin Vatican da ke kasar Rome ta yaba da irin aikin da Bishof Matthew Hassan Kukah ya ke yi wajen kare hakki da ‘yancin Bil Adama a Duniya.

Jorge Mario Bergoglio ya nada babban limamin darikar katolika na Sokoto, Matthew Hassan Kukah cikin majalisar masu gwagwarmayar kare al’umma.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa sanarwar wannan mukami ta fito ne daga bakin Mai magana da yawun bakin limamin Najeriyar, Christopher Omotosho.

Rabaren Christopher Omotosho ya bayyana cewa wannan karin girman da mai gidansa ya samu ta tabbata ne a wata takarda da aka aiko masa a makon da ya wuce.

KU KARANTA: Likitan Fafaroma ya mutu bayan jinyar COVID-19

Shugaban wannan majalisa da Hassan Kukah ya samu shiga, Peter Cardinal Turkson, shi ne ya sa hannu a takardar da ta fito a ranar 11 ga watan Junairu, 2021.

Peter Turkson ya ce da wannan matsayi, Matthew Kukah zai shiga cikin masu ba jagoran na darikar Katolika, Fafaroma, shawara a kan hakkin Bil Adama.

Ana zakulo wadanda za su zama masu ba Fafaroman shawara ne daga kowane bangare a Duniya.

Jawabin ya bayyana cewa Faston zai rike wannan kujera na tsawon shekaru biyar. Akwai yiwuwar a sabunta matsayin na sa nan gaba, inji Peter Turkson.

Matthew Hassan Kukah zai rika ba Fafaroma shawara a kan hakkin Bil Adama
Matthew Hassan Kukah da Fafaroma Jorge Mario Bergoglio Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Fafaroma ya yi Allah-wadai da yankan ragon da aka yi wa Manoma a Borno

Aikin Kukah da ‘yan majalisarsa sun hada da ba Fasto shawarwari a game da sha’anin safarar mutane, kare hakkin Bil Adama, adalci da kawo zaman lafiya.

A ranar kirismetin 2020, Fasto ya yi wani jawabi wanda ya bar baya da kura, ana zarginsa da taba addinin musulunci da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Limamin na Sokoto, Matthew Hassan Kukah ya zargi gwamnatin APC da nuna son kai wajen mulki.

A dalilin haka kungiyar Muslim Solidarity Forum ta ragargaji Mathew Hassan Kukah, ta ce akwai rashin son gaskiya a kalaman da Faston ya yi a bikin kirismeti.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel