Buhari: A canza hafsun sojoji da dabarun inganta tsaro Inji Gwamna Nyesom Wike
-Gwamna Nyesom Wike ya yi kira a canza shugabannin tsaro na Najeriya
-Gwamnan ya yaba da namjin kokarin da hafsun sojojin kasar suke kan yi
-Wike yace akwai bukatar gwamnati ta kawo sababbin jini da dabarun yaki
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta canza hafsun sojoji, sannan ta sauya dabarun yaki da tsageru a Najeriya.
Nyesom Wike ya bayyana cewa wannan sauyi zai taimaka wajen kawo sababbin jini da za suyi maganin matsalar rashin tsaron da ya dabaibaye al’umma.
Jaridar The Nation tace gwamnan ya yi wannan kira ne a ranar Juma’a, 15 ga watan Junairu, 2020, wajen bikin tunawa da dakarun sojoji na shekarar bana.
Mai girma gwamnan ya yaba da kokarin da shugabannin jami’an tsaro suke yi wajen yaki da ‘yan ta’adda, amma ya ce aiki ya yi wa dakarun sojojin yawa.
KU KARANTA: Sojoji sun kashe Miyagu da Boko Haram 2, 403 a bara - Buhari
A cewar Nyesom Wike, ‘yan ta’adda da miyagun ‘yan bindiga suna cigaba da kashe Bayin Allah.
Wike yake cewa ya kamata kowa ya damu da yadda sha’anin tsaro yake cigaba da tabarbarewa, don haka ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tashi tsaye.
“Iyaka karfin jami’an tsaro, iyaka karfin kasa. Gazawarta wajen kawo karshen Boko Haram duk da shekaru ana artabu, ya nuna akwai matsala da dabarunmu.”
Gwamnan ya kara da: “Mun godewa hafsun sojoji da kokarin da suka yi zuwa yanzu a filin daga. Amma muna tare da sauran al’umma da abin ya kai su bango.”
KU KARANTA: Dakarun Amotekun sun kashe mutane 11 a Oyo
“…Su bada wuri ga sababbin jini da tunani da za ayi wannan yaki, domin tabbatar da murkushe Boko Haram da ‘yan bindiga, su zama babu labarinsu a ban kasa.”
Dazu kun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gamu da mummunan martani bayan ya ce ana samun tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas.
Tsohon ‘dan majalisar tarayya a lokacin jamhuriya ta biyu, Dr. Junaid Muhammad, ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta gaza kare al'umma.
Junaid Mohammed yace karya shugaban kasa Buhari kurum zai tayi wa jama'a har ya kammala mulki.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng