2023: Tsofaffin Shugabannin Majalisun Ondo da Ekiti sun karyata goyon bayan Tinubu

2023: Tsofaffin Shugabannin Majalisun Ondo da Ekiti sun karyata goyon bayan Tinubu

- Tsofaffin shugabannin majalisun Ondo da Ekiti sun musanya ba Bola Tinubu goyon baya

- ‘Yan siyasar sun fito sun ce ba su yi alkawarin za su goyi bayan takarar Tinubu a 2023 ba

- Jiga-jigan APC sun ce suna tare da duk wanda jam’iyya ta tsaida masu a zabe mai zuwa

Tsofaffin shugabannin majalisun dokoki na jihohin Ondo da Ekiti, sun nesanta kansu daga mubaya’ar da ake rade-radin sun yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Jaridar Vanguard ta rahoto tsofaffin shugabannin majalisar wadannan jihohi biyu suna cewa ba suyi alkawarin mara wa Asiwaju Bola Tinubu baya a zaben 2023 ba.

Wadannan ‘yan siyasa sun bayyana cewa sun halarci taron da Rt. Hon. Mudashiru Obasa ya kawo maganar, amma ba su tsaida cewa zasu goya wa Bola Tinubu baya ba.

Wannan jawabi ya fito ne ta bakin tsofaffin shugabannun majalisar Ondo, Rt. Hons. Victor Olabimtan, Oluwasegunota Bolarinwa, Ayo Agbomuserin, Abdusalam Olawale Taofeeq, Kenneth Olawale.

KU KARANTA: Akwai yarjejeniya tsakanin Buhari da Tinubu a kan takarar 2023

Haka zalika tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Ekiti, Rt. Hon. Patrick Ajigbolamu ya yi tarayya da su a wannan matsaya da suka fitar a ranar Litinin.

‘Yan siyasar sun bayyana cewa sun halarci taron ne a dalilin shugaban kungiyarsu ta tsofaffin shugabannin majalisar jihohin Kudu maso yamma, Rt. Hon. Titi Oseni.

A jawabin na su, sun bayyana cewa Mudashiru Obasa ya nemi ‘yan siyasar su bada goyon bayansu ga Asiwaju Bola Tinubu a jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023.

Manyan ‘yan siyasar sun tabbatar da cewa sun shaida wa Mudashiru Obasa ba za su yi wa Bola Tinubu alkawari ba, za su jira su ji matakin da jam’iyya ta dauka.

KU KARANTA: Tinubu ya aika Akande su roka masa Buhari - Bode George

2023: Tsofaffin Shugabannin Majalisun Ondo da Ekiti sun karyata goyon bayan Tinubu
Asiwaju Tinubu Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Su ka ce “Gwamna Akeredolu na Ondo da Fayemi na Ekiti ne su ka fi dacewa su yi magana game da jihohinsu. Mun fada masu Tinubu ya na damar da zai nemi takara.”

Jawabin ya ce kowace jiha a Kudu maso yamma; Legas, Ondo ko Ekiti, ta cancanci ta fito da ‘dan takara, duk wanda jam’iyya ta ke so (Tinubu ko Fayemi), za mu bi shi.

A baya mun kawo maku rahoto cewa manyan ‘Yan siyasar Kasar Yarbawa sun fito sun bayyana cewa za su marawa takarar Bola Tinubu baya a babban zaben 2023.

Ana tunanin cewa takarar tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu a zaben 2023, zai samu kwarin-gwiwa da wannan rade-radi na samun goyon bayan 'ya 'yan APC.

Magoya bayan Tinubu sun rantse babu wanda zai hana gwaninsu ya gaji Muhammadu Buhari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng