PDP: Rochas Okorocha ya shigo Jam’iyyar mu, ka da ya maimata kuskuren 2014

PDP: Rochas Okorocha ya shigo Jam’iyyar mu, ka da ya maimata kuskuren 2014

- Rochas Okorocha ya na ta maganar kafa wata sabuwar tafiyar siyasa a 2023

- Jam’iyyar PDP ta kira gwamnan ya dawo cikinta a maimakon ya yi wannan

- Ta ce Sanatan zai maimaita kuskuren baya idan su ka kafa sabuwar jam’iyya

A ranar Litinin, 18 ga watan Junairu, 2021, aka ji Sanata mai wakiltar yammacin jihar Imo, Rochas Owelle Okorocha, ya na kara sukar jam’iyyar APC.

Jaridar Punch ta rahoto Sanata Rochas Okorocha yana cewa anyi gaggawan kafa jam’iyyar APC da nufin ta karbe mulki daga hannun PDP a zaben 2015.

Tsohon gwamnan na jihar Imo, ya bayyana cewa shi da wasu ‘yan siyasa masu tunani irin na sa, suna yunkurin kafa wata sabuwar tafiyar siyasa a kasar.

Daga jin wadannan maganganu, jam’iyyar hamayya ta PDP ta fito tana rokon ‘dan siyasar ya yi watsi da jam’iyyarsa ta APC mai mulki, ya shigo cikinta.

KU KARANTA: "Tinubu: Za mu goyi bayan duk wanda APC ta tsaida a 2023"

Jam’iyyar PDP ta ba tsohon gwamnan shawara ya sauya-sheka zuwa bangaren adawa, a maimakon ya sake yin irin kuskuren da ya yi a shekarar 2014.

A wata hira da aka yi da sakataren yada labarai na PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya ce sun ji dadin yadda irinsu Okorocha suka gane APC ta yaudari al’umma.

“Shawararmu ga mutane irinsu Rochas Okorocha shi ne ya guji maimaita kuskuren da ya yi sau biyu, domin duk jam’iyyar da aka kafa cikin gaggawa, za ta kife.”

“Ya tsallako PDP, jam’iyyar da take da tsari da tarihin yin aiki. Mun yi wasu kura-kurai a baya, kuma mun koyi darasinmu.” Inji Kola Ologbondiyan.

PDP: Rochas Okorocha ya shigo Jam’iyyar mu, ka da ya maimata kuskuren 2014
Rochas Okorocha Hoto: Twitter Daga: @realRochas
Source: Twitter

KU KARANTA: “Zamu karbe Jihar Adamawa da Anambra a zabukan 2021, 2023” Inji APC

Jami’in jam’iyyar yace akwai bambanci tsakanin PDP mai kaunar talaka, da kuma jam’iyyar da aka kafa tun asali da haushin wasu ‘yan siyasa domin ta karbe mulki.

A ranar Litinin, 11 ga watan Junairu, 2021 ne Sanata Rochas Okorocha ya ziyarci Ribas, ya kaddamar da hanyar da gwamna Nyesom Wike na jam'iyyar PDP ya yi.

Tun a wancan lokaci aka ji Sanatan na yammacin jihar Imo ya na kiran kafa wata sabuwar jam'iyya.

Sanata Rochas Okorocha ya bayyana cewa akwai bata-gari a APC da PDP, don haka ya ba masu kishin Najeriya shawara su daina magiya, su hada-kai, su ceto jama'a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel