COVID-19: Gwamnonin Jihohi za suyi zama domin a samu mafita a Najeriya

COVID-19: Gwamnonin Jihohi za suyi zama domin a samu mafita a Najeriya

- Kungiyar Gwamnoni ta kira taro ganin yadda cutar COVID-19 ta ke kara yaduwa

- Gwamnonin kasar za suyi zama domin rage yaduwar Coronavirus a fadin jihohi

- Abdulrazaque Bello-Barkindo ne ya bada wannan sanarwa a madadin NGF a jiya

Gwamnonin jihohi 36 da ke tarayyar Najeriya za su yi taronsu na 23 ta kafar yanar gizo, da nufin kawo yadda za a rage yawan masu kamuwa da COVID-19.

Jaridar Punch ce ta fitar da wannan rahoto a jiya ranar Litinin, 19 ga watan Junairu, 2021.

Rahotanni sun bayyana cewa za ayi wannan zama ne a ranar Laraba, inda gwamnonin za su fito da matakan da za a bi domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Sanarwar wannan taro ta fito ne daga ofishin shugaban yada labarai da hulda da jama’a na ofishin kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdulrazaque Bello-Barkindo.

KU KARANTA: COVID-19 ba ta taba talaka?

Malam Abdulrazaque Bello-Barkindo ya bada wannan sanarwa ne ranar Litinin a garin Abuja.

Sanarwar ta ce: “Ganin yadda sabuwar nau’in COVID-19 ta ke yaduwa da karfi a Duniya, gwamnoni 36 suna shirin fito da matsaya, domin za suyi zama domin kawowa Najeriya mafita.”

“Wannan taro wanda shi ne na farko a shekarar nan ta 2021, zai kasance ta kafar yanar gizo kamar yadda aka saba, domin bin sharudan yaki da annobar COVID-19.”

Bello-Barkindo ya kara da cewa: “Wannan shi ne taro na 23 da kungiyar gwamnoni tayi ta yanar gizo. Za a fara taron ne da karfe 2:00 daidai. Ana sa ran gwamnoni su kitsa tun karfe 1:00”

KU KARANTA: Gwamnatin Ondo ta shigo da tsarin rajista, ta haramta kiwo a jeji

COVID-19: Gwamnonin Jihohi za suyi zama domin a samu mafita a Najeriya
Gwamnonin Jihohi a Aso Villa Hoto: Twitter Daga: @BashirAhmaad
Source: Twitter

“Shugaban gwamnonin da ke kula da harkar yaki da COVID-19, Ifeanyi Okowa, zai gabatar da takaitaccen bayani game da abin da ake bukatar sani game da rigakafin cutar.”

Sanarwar ta nuna cewa Dr. Ifeanyi Okowa, zai yi wa NGF jawabi a kan sabon samfurin cutar da ta bulla. Kayode Fayemi zai yi magana a kan ganawarsu da shugaban kasa.

A farkon makon nan kun samu labari cewa duk da umarnin gwamnatin tarayya ta bada na komawa karatu, babu maganar bude makarantu a fadin jihar Kaduna.

Ko da fwamnatin tarayya ta sa ranar da za a koma makaranta, ba za a bude makarantun jihar Kaduna ba kamar yadda gwamnatin Jihar ta bayyana a ranar Lahadi.

Za a cigaba da rufe duka sauran makarantu har da A.B,U Zaria saboda annobar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel