Duk da umarnin gwamnatin tarayya, babu maganar bude makarantu a Kaduna

Duk da umarnin gwamnatin tarayya, babu maganar bude makarantu a Kaduna

- Ko da Gwamnatin tarayya ta sa rana, ba za a bude makarantun jihar Kaduna ba

- Gwamnatin Jihar Kaduna tace KADPOLY da Open University kadai ne za a bude

- Za a cigaba da rufe duka sauran makarantu har da A.B,U Zaria saboda COVID-19

Ana sa ran a bude makarantu a Najeriya a ranar Litinin, 18 ga watan Junairu, 2021, bayan tsawon lokacin da aka dauka a gida saboda annobar COVID-19.

Amma a jihar Kaduna, gwamnatin Nasir El-Rufai ta ce za a cigaba da rufe duk wasu makarantun da ke jihar, har da manyan makarantun gwamnatin tarayya.

Jaridar Daily Trust tace Sakatariyar din-din-din na ma’aikatar ilmi na jihar Kaduna, Phoebe Sukai Yayi, ta bada wannan sanarwa a ranar Lahadi, 17 ga watan Junairu.

Phoebe Sukai Yayi ta bayyana cewa suna lura da yadda cutar COVID-19 ta ke cigaba da yaduwa a Kaduna.

KU KARANTA: Abin da ya hana COVID-19 yi wa Talaka tasiri

Babbar jami’ar ma’aikatar ilmin ta shaidawa manema labarai cewa gwamnatin Kaduna za ta fitar da matsaya game da lokacin da za a bude makarantun jihar.

A cewar Sakatariyar ta din-din-din, makarantu biyu kadai za a bude a yau 18 ga watan Junairu, 2021; Kaduna Polytechnic da National Open University.

Sukai Yayi ta ce wadannan makarantu na gaba da sakandare biyu sun nemi ma’aikatar ta ba su alfarmar bude wa domin dalibai su samu su rubuta jarrabawa.

Ko da gwanatin tarayya ta ce a bude makarantu, Yayi ta ce kawo yanzu babu ranar komawa karatu a Kaduna.

KU KARANTA: An roki Gwamnati ta dakatar da bude Makarantu

Duk da umarnin gwamnatin tarayya, babu maganar bude makarantu a Kaduna
Gwamnan Kaduna Hoto: Twitter Daga @GovKaduna
Asali: Twitter

“Muna so mu fada da babbar murya cewa jihar Kaduna ba ta sa ranar da za a bude makarantu ba.” Phoebe Sukai Yayi ta shaidawa ‘yan jarida a jiya da rana.

Za a cigaba da rufe har jami’ar ABU Zaria domin makarantar ba ta tuntubi ma’aikatar ilmi ba.

Za a rabawa Mata 160, 000 a fadin jihohin Najeriya 36 kudi domin tallafawa marasa galihu, musamman a lokacin da COVID-19 ta taba tattalin arzikin kasa.

Ministar tarayya, Sadiya Umar Farouk ta ce gwamnati ta zabi Mata 6, 000 da za a rabawa N20, 000 a Jihar Katsina.

Ministar bada tallafi da agajin gaggawa da cigaban al’umma tace wannan na cikin manufofin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na rage radadi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng