An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria
- Kasashen duniya, musamman a nahiyar Turai, sun yi matukar mamakin yadda annobar korona bata hallaka mutane da yawa a nahiyar Afrika ba
- Tsohon kakakin tsohon shugaban kasa Jonathan, Doyin Okupe, ya ce yana da kwafin wani rahoto da likitoci fiye da 100 suka sanyawa hannu
- A cikin rahoton, Okupe ya ce an alakanta karfin garkuwar jikin mutane da adadin sinadarin Vitamin D3 da ake samu daga hasken rana
Cif Doyin Okupe, kakakin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya wallafa wata makala akan rashin tasirin kwayar cutar korona a tsakanin talakawa mazauna nahiyar Afrika.
Okupe ya yi ikirarin cewa yana da kwafin rahoton wani bincike Wanda masana kimiyya suka gudanar.
A cikin rahoton, Okupe ya bayyana cewa masana kimiyya sun alakanta karfin garkuwar jikin mutane da sinadarin vitamin D3 wanda ake samu daga hasken rana, kamar yadda Punch ta rawaito.
Ya ƙara da cewa samun sinadarin Vitamin D3 na bada garkuwa da kuma rigakafin annobar COVID-19 kuma yawanci talakawa sun fi masu hali yawan wannan sinadarin.
KARANTA: Korona: NYSC ta hana taron ibada, ta daga ranar bude sansanin horo
Ƙasashen turawa na fama da ƙarancin wannan sinadarin na Vitamin D3 kuma rashin wannan sinadarin na taimakawa wajen ta'azzara da taɓarɓarewar annobar COVID-19 a jikin wanda ya kamu da cutar.
Hakazalika, koda an kamu da kwayar cutar COVID-19, shi wannan sinadarin yana rage raɗaɗin ciwon kuma yana taimakawa wajen warkewa da sauri.
A cewarsa, yana da kwafin wani daftari da manyan likitoci 120 suka sawa hannu kuma aka turawa shugabannin duniya akan su magance ƙarancin sinadarin Vitamin D3 a yankin Turai da Amurka wanda suke samun hasken rana na ƴan watanni a shekara, lamarin da yasa jama'ar yankin ke fama da ƙarancin sinadarin.
KARANTA: Korona 2.0: Za'a ji jiki a watan Janairu; NCDC ta gargadi 'yan Nigeria , ta fadi dalili
Da yawa daga cikin masu hannu da shuni a yankin Afrika na da ƙarancin sinadarin Vitamin D3 saboda basu cika shiga rana ba, kuma wannan shi ke bawa COVID-19 damar ɗana tarkonta akan su.
Wannan yana faruwa ne saboda abu ne mayuwaci ka ga masu hannu da shuni cikin rana; daga gida, sai Ofis, sai mota, ko ina kuma cikin na'ura sanyaya yanayi, acewarsa.
Duk da haka, zama a cikin hasken rana na mintuna 30 kacal na bada adadin kusan 20,000ICU na sinadarin Vitamin D3 a jikin mutum.
Wannan ne yasa matasa, ɗalibai, ƴan talla da ƴan kasuwa da sauran masu harkoki a cikin rana suke da garkuwar jiki mai ƙarfin gaske akan COVID-19.
Daga ƙarshe, Cif Okupe ya shawarci masu hannu da shuni da basa yin wani aiki a cikin rana da su daure su ware ko mintuna 20 ne domin yin tattaki a cikin rana don samun sinadarin Vitamin D3 da zai basu kariya daga COVID-19.
Ya kuma yi kira ga sauran al'umma da su bi matakan kare kai daga cutar COVID-19.
A ranar Alhamis ne Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta sabunta sharudan da makarantu zasu cika da matakan da zasu dauka bayan sun bude a ranar 18 ga watan Janairu.
Ministan ilimi, Adamu Adamu, a ranar Alhamis, 14 ga watan Janairu, ya sanar da cewa za'a bude makarantu kamar yadda aka tsara.
Ana shawartar Malamai su tabbatar dalibai sun nesanta da juna a ajuzuwansu tare da tilasta biyayya ga dukkan matakan kare kai.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng