Rotimi Akeredolu yace nan da mako daya, makiyaya su fice daga jejin Ondo

Rotimi Akeredolu yace nan da mako daya, makiyaya su fice daga jejin Ondo

- Gwamnan jihar Ondo ya tsaurara matakai domin yaki da garkuwa da mutane

- Rotimi Akeredolu ya ba makiyayan da suke Ondo kwanaki 7 su bar jejin jihar

- Gwamnatin Ondo ta haramta kiwon yamma da hawa manyan tituna daga yau

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, ya bada wa’adin mako daya ga makiyaya su bar kungurumin jejin da ke cikin jiharsa.

Mai girma gwamnan Ondo ya bada wannan wa’adi ne a yankurin da yake yi na kawo karshen matsalar garkuwa da mutane da sauran ta’adin da ake yi a jihar.

Sanarwar Rotimi Akeredolu ta fito ne kai tsaye a shafinsa na Twitter, a ranar Litinin 18 ga watan Junairu. 2021.

Rotimi Akeredolu a jawabin na sa yake cewa an maida jejin jihar Ondo wuraren tafka ta’adi, don haka a matsayinsa na gwamna ya dauki wannan mataki a yau.

KU KARANTA: Nasarorin da Sojojin kasa su ka samu a 2020 inji Buhari

Ya ce: “A yau, mun dauki babban mataki na kawo karshen matsalar garkuwa da mutane, da sauran danyen ayyukan da ake yi da muka samu labari a rahotonmu.

“Ana alakanta wadannan munanan abubuwa da wasu miyagu da ke fakewa da sunan makiyaya.” Inji gwamnan.

“Wadannan miyagu sun maida jejinmu wuraren ajiye wadanda suka yi garkuwa da su, suna tattauna yadda zasu karbi kudin fansa da yin sauran laifuffuka.”

Daga cikin matakan da aka dauka, za a bar duk wasu jeji nan da kwana bakwai. An kuma haramta kiwo da dare, sannan an hana dabbobi yawo a manyan tituna.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta ce a bude makarantu, El-Rufai ya hana

Rotimi Akeredolu yace nan da mako daya, makiyaya su fice daga jejin Ondo
Gwamna Rotimi Akeredolu Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Gwamna ya kuma hana kananan yara kiwo, sannan bayan wannan wa’adin ya cika, gwamnati za ta bada damar duk mai bukatar yin kiwo, ya yi rajista da hukuma.

A yau ne kuma muke samun labari cewa hedikwatar tsaro cewa ‘yan bindigan da ke ta’adi a Zamfara, sun gane ba su da wayau a hannun dakarun sojojin kasa.

Janar John Enenche ya ce dakarun Sojoji sun yi wa ‘Yan bindiga rugu-rugu a dajin Zamfara.

Sojojin Najeriya na Operation Hadarin Daji sun kashe tsageru 35 a dajin yankunan Bungudu da Muradun a jihar Zamfara, har sun karbe wasu dabbobi da aka sace.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng