Tinubu ne ya aikasu su roki Buhari; Bode George ya fadi dalilin ziyarar dattijan APC zuwa Villa

Tinubu ne ya aikasu su roki Buhari; Bode George ya fadi dalilin ziyarar dattijan APC zuwa Villa

- Gumurzun siyasa tsakanin dattijon jam'iyyar PDP, Bode George, da abokin karawarsa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu,ya sake ɗaukar zafi

- George ya sake kunno wutar rikicin ne bayan ya yi iƙirarin cewar ziyarar da jiga-jigan dattijan jam'iyyar APC suka kai Villa sun yi ne a madadin Tinubu

- Duk da Tinubu bai maida martanin bisa iƙirarin ba, ɗaya daga cikin shugabannin APC ya yi watsi da iƙirarin nasa

Chief Bode George, babban jigo a jam'iyyar PDP a kudu maso yamma, ya maida martani a kan ziyarar da shugabannin jam'iyyar APC suka kaiwa shugaban ƙasa a fadarsa ta Aso rock ranar Juma'a.

Tsofaffin gwamnonin Jihohin Ogun da Osun, Chief Segun Osoba da Chief Bisi Akande, da sauran jiga jigan jam'iyyar APC a ranar Juma'a, 20 ga Nuwamba, sun kaiwa shugaban ƙasa ziyara a fadarsa.

Duk da ba'a bayyana maƙasudin taron ba, George, a martaninsa, ya yi iƙirarin cewa taron anyi shi ne saboda jagoran jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, kamar yadda jaridar The Guardian ta rawaito.

KARANTA: Atiku ya fadi daliin da yasa tattalin arzikin Nigeria ke karyewa a karkashin mulkin Buhari

Ya ce taron bashi da wata manufa bayan abinda ya bayyana ƙarara duk da akwai ɓoyayyar manufa, inda ya yi iƙirarin cewa rashin ganin fuskar Tinubu yayin taron ya tabbatar an yi taron ne akansa.

Tinubu ne ya aikasu su roki Buhari; Bode George ya fadi dalilin ziyarar dattijan APC zuwa Villa
Tinubu ne ya aikasu su roki Buhari; Bode George ya fadi dalilin ziyarar dattijan APC zuwa Villa @Bashirahmad
Asali: Twitter

Ya ƙara da cewa taron anyi shi ne don "don sauƙaƙawa Tinubu da nemar masa afuwa".

Jigon na jam'iyyar PDP ya shawarci Buhari a kan kar ya yarda ya faɗa tarkon wanda zasu sauya asalin batun da ke damun jihar Legas domin biyan bukatar kansu da wasu tisararun mutane.

KARANTA: Gwamnatin tarayya ta kammala shirin zabge harajin motoci da kaso biyar

Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP ya ce akwai bukatar Tinubu ya biya bashin makudan kudaden da ya wawushe daga aljihun jihar Legas.

A rahoton da jaridar Nigerian Tribune ta wallafa, ta bayyana cewa George ya yi yunƙurin mamaye siyasar jihar Legas, wanda hakan yasa shi bada gudunmawa ga zanga zangar EndSARS, musamman a Lekki tollgate.

Legit.ng Hausa ta rawaito Farfesa Sahabi Ɗanladi Mahuta, jigo kuma uba a jam'iyyar APC, shararren malamin addinin Musulunci na cewa ba zasu taba lamunta a dauki Kirista daga arewa a matsayin dan matakarar mataimakin shugaban kasa ba.

Mahuta, Farfesa a fannin kimiyyar sinadaran halittu (Biochemistry) a jami'ar Usman Ɗanfodiyo, Sakkwato, ya bayyana hakan ne jimkadan bayan kammala wani taron jagororin addinin Musulunci a Abuja.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng