Shugabannin Majalisan Jihohin Kudu sun hadu a kan takarar Bola Tinubu a 2023

Shugabannin Majalisan Jihohin Kudu sun hadu a kan takarar Bola Tinubu a 2023

- Jiga-jigan ‘yan siyasa suna ta gyara lissafinsu tun kafin zaben 2023 ya karaso

- An samu wadanda suke goyon bayan Bola Ahmed Tinubu ya fito Shugaban kasa

- Shugabannin Majalisa na Jihohin Kudu maso yamma suna tare da Bola Tinubu

Daily Trust ta ce takarar tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023, ya samu kwarin-gwiwa a jiya Alhamis, 14 ga watan Junairu, 2020.

Rahotanni sun bayyana cewa tsofaffin shugabannin majalisar dokoki masu-ci, sun yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mubaya’a domin ya yi takara a 2023.

Wadannan shugabannin majalisar dokoki sun fito ne daga jihohin Kudu maso yammacin Najeriya.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da magoya-bayan babban jigon na jam’iyyar APC mai mulki su ke ganin cewa wasu ‘yan siyasa suna yi wa gwaninsu adawa.

KU KARANTA: Fastocin Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai da Bola Tinubu sun fito

Magoya bayan na Bola Ahmed Tinubu sun rantse cewa babu wani abu ko wani ta’aliki da ya isa ya hana ‘dan siyasar ya gaji Muhammadu Buhari a 2023.

Tinubu ya samu wannan goyon baya ne a wajen wani taro da shugaban majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya gabatar da gidauniyarsa BAT.

Rt. Hon. Mudashiru Obasa ya gabatar da Bola Ahmed Tinubu (BAT) Foundation wajen wani taro na ‘yan majalisa, inda ya bayyana masu nasarorin wannan tafiyar.

Obasa ya tabbatar da cewa Tinubu bai bayyana cewa ya na sha’awar kujerar shugaban kasa ba.

KU KARANTA: An bar Tinubu ya na tsilla-tsilla, bangaren CPC ta rike APC

Shugabannin Majalisan Jihohin Kudu sun hadu a kan takarar Bola Tinubu a 2023
Bola Tinubu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A karshen zaman, shugabannin majalisar sun yarda cewa Tinubu a matsayinsa na Bayarabe wanda ya san kan aiki, ya fi kowa dacewa ya shugabanci Najeriya.

Ko da mun sha jaddada cewa Bola Tinubu bai taba furta cewa zai nemi takarar shugaban kasa a Najeriya ba, amma wasu da dama suna yi masa harin kujerar.

Kwanaki kun ji cewa wata kungiyar siyasa da ta ke tare da Asiwaju Bola Tinubu ta bayyana cewa ta samu masoya miliyan guda da su ke goyon bayan muradunta.

Wannan kungiya da wasu takwarorinta suna hurowa tsohon gwamnan Legas ya yi takara a 2023.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel