SERAP ta bukaci a haramtawa Gwamnatin tarayya saida kadarorin kasa a 2021
- SERAP ta rubutawa ‘Yan Majalisa takarda a kan shirin saida kadarorin kasa
- Kungiyar ta na ba Majalisa shawara ta hana ayi gwanjon kadarorin Najeriya
- Idan har ‘Yan Majalisa ba suyi wani abu a kai ba, SERAP za ta iya shiga kotu
Kungiyar SERAP mai kare hakkin ‘yan kasa, SERAP, ta yi kira ga shugabannin majalisar tarayya, suyi maza su sake duba kundin kasafin shekarar 2021.
SERAP ta rubutawa Rt. Hon. Femi Gbajabiamila da Sanata Ahmad Lawan takarda, su dakatar da gwamnatin tarayya daga saida kadarorin kasa a shekarar nan.
Vanguard tace kungiyar ta bayyana wannan ne a wata wasika da ta rubuta a ranar 16 ga watan Junairu, 2021, ta bakin mataimakin darektanta, Kolawole Oluwadare.
Mista Kolawole Oluwadare ya tuna wa majalisar tarayya cewa a kundin tsarin mulki, nauyin sa ido a kan abin da gwamnati take yi, ya rataya ne a kanta.
KU KARANTA: Buhari ya isa majalisar tarayya da kundin kasafin kudin 2021
Kolawole Oluwadare ya ba shugabannin majalisar shawara su duba yadda za a rage facaka da kudi ba tare da an kai ga saida kadarorin da Najeriya take ji da su ba.
Daga cikin shawarwarin da shugaban kungiyar ya bada shi ne a rage albashi da tulin alawus da ake biyan ‘yan majalisar tarayya da ma’aikatan fadar shugaban kasa.
“Kyale gwamnati ta saida kadarorin kasa, sannan a karbo bashi domin aiwatar da kasafin kudin 2021, ya na nufin sabawa kundin tsarin mulki.” Inji SERAP.
“Saida kadarorin da ake ji da su domin samun kudi a kasafin 2021, zai zama tafka da warwara a lokacin da ake kokarin kawo karshen facaka da rashin gaskiya.”
KU KARANTA: Duk da kiran babu-babu: Gwamna zai ba tsofaffin Gwamnoni da Mataimaka N10bn
Wannan kungiya ta bukaci a hana gwamnati cin bashi idan ba za ta fadi abin da take yi da kudin da ta aro ba. SERAP tace idan majalisa ta ki daukar mataki, za ta tafi kotu.
Gwamnatin tarayya da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake jagoranta ta yi niyyar saida wasu kadarorin da kasa ta mallaka domin aiwatar da ayyuka.
A jawabinsa na sabuwar shekara, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan Najeriya su kwantar da hankulansu saboda zai farfado da tattalin arzikin kasa.
Gwamnatin Buhari tace za ta dauke hankalin al'ummar kasa daga man fetur zuwa aikin noma.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng