Muhimman Abubuwa 5 da Buhari ya fada a jawabinsa na sabuwar shekara

Muhimman Abubuwa 5 da Buhari ya fada a jawabinsa na sabuwar shekara

Yayinda yan Najeriya ke murnan sabuwar shekara, shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga al'ummarsa da safiyar Juma'a, 1 ga watan Junairu, 2021.

Shugaban kasan ya jaddada alkawuran da yayiwa yan Najeriya a jawabinsa, inda ya tabbatar da cewa lallai an ji jiki a 2020.

A jawabinsa, shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta farfado da tattalin arzikin Najeriya kuma za tayi yaki da cin hanci da rashawa.

Hakazalika ya yi alkawarin kare rayukan yan Najeriya da dukikoyiyinsu.

Legit ta tattaro muku muhimman abubuwan da ya fada:

1. Ya yi alkawarin kawo karshen rashin tsaro

Shugaban kasan ya jaddada cewa zai yi garambawul cikin lamarin tsaro a 2021.

A cewarsa, za'a karawa Sojoji da yan sanda kaimi domin dakile yan bindiga a ciki da wajen kasa.

2. Jaddada niyyar cika alkawarin da ya yiwa matasan Najeriya

Shugaban kasan ya jaddada niyyar cika alkawura biyar da ya yiwa matasan Najeriya sakamakon zanga-zangan #EndSARS.

Ya ce gwamnatinsa ta saurari bukatar matasan Najeriya.

KU DUBA: Allah ya yi wa Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu rasuwa

Muhimman Abubuwa 5 da Buhari ya fada a jawabinsa na sabuwar shekara
Muhimman Abubuwa 5 da Buhari ya fada a jawabinsa na sabuwar shekara Hoto: Femi Adesina
Source: Facebook

KU KARANTA: Bayan rusa gudan, an damke wadanda suka shirya casun tsiraici a jihar Kaduna (Hotuna)

3. Tattalin arzikin Najeriya

Shugaba Buhari a jawabinsa ya bukaci yan Najeriya su kwantar da hankulansu saboda zai farfado da tattalin arzikin kasar ta hanyar dauke hankalinmu daga man fetur zuwa aikin noma domin samun isasshen abinci.

Ya yi bayanin cewa wannan gwamnatin na ayyuka daban-daban domin samawa matasa aikin yi da taimakawa kananan yan kasuwa.

4. Yaki da rashawa

Shugaban kasan ya kara da cewa Najeriya ta samu riba a yakinta da rashawa kuma a wannan sabuwar shekara gwamnatinsa zata kawar da rashawa.

5. Annobar Korona

Shugaba Buhari ya zayyana kokarin da gwamnatinsa tayi domin sayan rigakafin Korona ga yan Najeriya.

A cewarsa, gwamnatin ta lashi takobin kiyaye kasar da waiwayen annobar Korona ta biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel