Yanzu-yanzu: Buhari ya dira majalisar dokokin tarayya don gabatar da kasafin kudin 2021

Yanzu-yanzu: Buhari ya dira majalisar dokokin tarayya don gabatar da kasafin kudin 2021

- Shugaba Buhari da manyan mukarranbansa sun shiga zauren majalisa

- An shirya fara zaman gabatar da kasafin kudin misalin karfe 11 na safe

Kamar da aka shirya, Shugaba Muhammadu Buhari ya dira zauren majalisar dokokin tarayya domin gabatar da kasafin kudin Najeriya na shekarar 2021 a ranar Alhamis.

Yan Najeriya sun dasa kunne domin jin irin abubuwan da shugaba Buhari ya shirya yiwa yan Najeriya a shekarar 2021.

Daga cikin abubuwan da ake sa ran jin shine adadin kudin sabbin ayyukan da gwamnatin Buhari ta shirya yi a 2021, farashin da gwamnati zata sayar da danyan mai, adadin basussuka da aka shirya karbowa, da kudin basussukan da za'a biya.

Sauran sune adadin kudin shigan da ake sa ran samu ta wasu hanyoyi sabanin man fetur irinsu haraji.

DUBA NAN: Masu zanga-zanga sun yi wa hedkwatar 'yan sanda zobe a Abuja

Yanzu-yanzu: Buhari ya dira majalisar dokokin tarayya don gabatar da kasafin kudin 2021
Hoto daga @tvcnewsng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Allah ya yi wa shugaban NULGE, Ibrahim Khalil rasuwa

A ranar Talata, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar da shugaba Buhari ya aikewa majalisar.

A baya mun kawo muku rahoton cewa majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) wacce shugaban kasa Muhammadu Buhari yake jagoranta a taronta na yau Laraba, ta amince da fitar da tiriliyan N13.08 a matsayin kasafin shekarar 2021.

Ministan kudi, kasafi da tsarin kasa, Hajiya Zainab Ahmed ce ta sanar da hakan a wani taro na manema labarai akan abinda majalisar zartarwar ta zartar a taron da aka yi a wani dakin taro dake fadar shugaban kasa, Abuja.

Hajiya Zainab tare da Minsitan yada labarai da al'adu, Lai Muhammed; karamin Ministan kasafi, tsari da tattali, Clement Agba da darakta janar na ofishin kasafin kasa, Ben Akabueze ne suka yi bayanin.

Ministan tace gaba daya kasafin shekarar ya kama tiriliyan N2.083, yayin da kudin kowacce gangar man fetur ake tammaninsa a dala 40, Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel