Kungiyar Bilbao ta yi waje da Madrid, ta doke Barcelona, ta dauki kofin Super Cup

Kungiyar Bilbao ta yi waje da Madrid, ta doke Barcelona, ta dauki kofin Super Cup

- Athletic Bilbao tayi galaba a kan Barcelona a wasan kofin Spanish Super Cup

- Lionel Messi ya samu jan katinsa na farko ya na mai dauke da rigar Barcelona

- Messi ya taba samun jan kati sau biyu, amma lokacin da yake bugawa kasarsa

Tauraro Lionel Messi ya buga wa kungiyar Barcelona wasanni 750, amma sai yanzu ne ya samu jan kati a wasan kungiyar ta sa da Athletic Bilbao.

Lionel Messi ya samu jan katinsa na farko a cikin rigar Barcelona ne a wasan cin kofin Spanish Super Cup wanda aka buga a ranar Lahadi, 17 ga watan Junairu.

Goal.com ta ce da farko Alkalin wasa, Gil Manzano, bai ga danyen aikin da Messi ya yiba, sai daga baya ya duba bidiyon VAR, ya ba ‘dan wasan jan kati nan-take.

Wannan wasa bai yi wa Barcelona dadi ba, ta sha kashi 2 – 3 a hannun kungiyar ta Athletic Bilbao.

KU KARANTA: Kul Messi ya bar Barcelona - Fasto

Kungiyar Bilbao ta yi waje da Madrid, ta doke Barcelona, ta dauki kofin Super Cup
Messi Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Nasarar da Bilbao ta samu tana nufin ta lashe wannan gasa na karamin kofi. Kafin nan kungiyar tayi galaba a kan bangaren Zinedine Zidane, Real Madrid.

Antoine Griezmann ya zurawa Barcelona kwallaye biyu, amma ‘yan wasa Oscar de Marcos da Villalibre suka rama, ta biyun ta zo ne daf da za a tashi wasan.

Bayan an tafi karin lokaci ne kuma Iniaki Williams ya zurawa Barcelona kwallo ta uku a raga. A minti na 121, aka kori Tauraro Lionel Messi daga filin kwallon.

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar FA ta Sifen za ta iya dakatar da Lionel Messi na tsawon wasanni hudu saboda wannan laifi da ya yi a daren jiya.

KU KARANTA: Messi ya yi kaca-kaca da Kungiyar Barcelona a kan tashin Luis Suarez

Idan haka ta tabbata, Barcelona da ta ke matsayi na uku a La-liga za ta buga wasanninta da Elche, Athletic Club da Real Betis da Copa Del Rey babu Tauraron.

Idan za ku tuna, bayan shekaru 16 a kulob, a 2020 ne Lionel Messi ya shaida wa ƙungiyar Barcelona cewa yana son barin kungiyar kwallon kafar.

Kungiyar ta tabbatar da cewa ɗan wasan na ƙasar Argentina, Lionel Messi, ya rubuta mata wasika cewa yana son ya tashi, ya koma buga kwallo a wata kungiyar.

Daga baya Messi wanda ya lashe Ballon d'Or har shida ya hakura ya cigaba da zama Barcelona.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel