Shishigi: Fasto T.B Joshua ya shawarci Messi a kan shirin barin kungiyar Barcelona
Jagora kuma babban fasto a Cocin SCOAN (Synagogue Church of All Nations), Fasto T.B Joshua, ya shawarci kaftin din kungiyar Barcelona, Lionel Messi, a kan tababar da ta kunno kai a tsakaninsa da mahukuntan kulob din Barca.
Har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta na kokarin ganin cewa ta shawo kan Messi ya sauya ra'ayinsa na son sake yin aiki da tsohon maigidansa kuma kociyan kulob din Mancester City, Pep Guardiola.
Sharudan kwantiragin Messi a Barcelona sun nuna cewa sai ya biya kungiyar wasu makudan kudade matukar ya na son ya sauya kulob a kakar wasa ta bana da za a fara kwanan nan.
Messi, haziki kuma fitaccen dan wasan kwallon kafa mai shekaru 33, ya shafe kusan shekaru 20 ya na bugawa kungiyar Barcelona wasa.
Amma a makon da ya gabata, Messi, kaftin a kungiyar kwallon kafa ta kasar Argentina, ya bayyana cewa zai bar Barcelona duk da har yanzu kungiyar ta kafe a kan cewar shine kaftin dinta.
Alamu sun nuna cewa dan wasan da gaske yake yi a kan niyyarsa bayan ya ki halartar atisayen motsa jiki da sabon kociyan Barcelona, Ronald Koeman, ya kira 'yan wasan kungiyar ranar Litinin.
A ranar Laraba ne mahaifin Messi da wakilinsa suka dira a kasar Spain domin tattaunawa da shugaban kulob din Barcelona, Josep Maria Bartomeu, a kan barakar da ta kunno kai tsakanin Messi da kungiyar Barca.
DUBA WANNAN: Sakon Buhari ga 'yan Najeriya a kan tsadar kayan abinci
Da ya ke tofa albarkacin bakinsa a kan wannan balahira a shafinsa na tuwita, TB Joshua ya bukaci Messi a kan kar ya bar kungiyar Barcelona cikin fushi da bacin rai.
Sakon TB Joshua na cewa;
"Ba shawara ce mai kyau ba a ce Lionel Messi ya bar Barcelona cikin fushi da bacin rai. Ba zai yiwu a kulla zumunci ko wata alaka ta kirki da mutumin da aka yi rabuwar baran-baran da shi ba. Wanna ita ce shawarar da zan bawa Messi. Tarihi zai mana hukunci," kamar yadda ya wallafa.
Tuni kafafen yada labarai su ka bayyana cewa an fara kulla yarjejeniyar kwantiragi a tsakanin kungiyar Machester City da Messi tun kafin ya yi sallama da kungiyar Barcelona.
Har yanzu akwai ma su ganin cewa za a iya daidatawa tare da yin sulhu tsakanin Barcelona da Messi, dan wasan da kungiyar bata taba samun kamarsa ba a baya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng