Yanzu-yanzu: Messi ya ce zai bar Barcelona

Yanzu-yanzu: Messi ya ce zai bar Barcelona

Bayan kimanin shekaru 20, Lionel Messi ya shaida wa ƙungiyar Barcelona cewa yana son barin kungiyar.

Kungiyar ta tabbatar a ranar Talata cewa ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Argentina ya rubuta mata wasika cewa yana son ya tafi.

Sanarwar na zuwa ne kimanin kwanaki 11 bayan kayan da ƙungiyar ta sha na 8 - 2 a hannun Bayern Munich, daya daga cikin kaye mafi muni a tarihin kwallon ƙafa.

Wannan shan kayen ya ƙara wa kungiyar abin takaici - duba da cewa tun 2007-08 ba su ci kofi ba ga shan kaye kamar yadda Sky reports ta ruwaito.

Messi ya lashe Ballon d'Or guda shida yayin zamansa a Barcelona a matsayin ɗan wasan daga cikin mafi girma a duniya.

Yanzu-yanzu: Messi ya ce zai bar Barcelona
Yanzu-yanzu: Messi ya ce zai bar Barcelona. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda tsohon minista ya 'zazzagi' dan jarida saboda ya masa wata tambaya

Ya kuma taimaka wa kungiyar ta lashe kofin gasar wasar ƙwallon ƙafa na Spain guda 10 da gasar ƙwallon wasan 'Champions League' hudu.

A wani labari na daban, tsohon shugaban kungiyoyin kwallon kafa ta Gombe, Shuaib Gara-Gombe ya bayyana cewa Aisha Buhari, matar Shugaba Muhammadu Buhari ta so a nada tsohon dan wasan Super Eagles, Daniel Amokachi a matsayin ministan wasanni.

ranar 20 ga watan Agusta ne Buhari ya nada tsohon dan wasan na Everton a matsayin mataimakinsa na musamman a bangaren wasanni, watanni kadan bayan an nada shi jakadar wasanni na kasar.

Gara-Gombe, yayin hira da aka yi da shi a gidan rediyo na Kennis 104.1 FM a ranar Litinin ya ce, "Aisha Buhari ta dade tana fafutikan ganin an saka wa wadanda suka bada gudun mawa yayin yakin neman zaben mijinta, ta dade tana neman a saka wa Amokachi.

"Hasali ma, Ministan wasanni ta so a nada Amokaci, amma hakan bai yi wu ba, da aka cigaba da yi wa fadar shugaban kasa matsin lamba kan batun, sai Buhari ya nada shi wakilin wasan kwallo.

Bayan nadin an ce ya rika aiki karkashin Sunday Dare. Amma kawai zuwa maaikatar ya ke yi baya aikata komai bayan nadinsa a matsayin wakilin kwallon kafa.

"Ya kamata a yi wa Amokaci sakayya. Buhari bai san Amokaci ba, amma Buhari ya san matarsa wacce ita kuma ta yi aiki tare da Amokachi a lokacin yakin neman zabensa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel