Lionel Messi ya yi kaca-kaca da Kungiyar Barcelona a kan saida Luis Suarez

Lionel Messi ya yi kaca-kaca da Kungiyar Barcelona a kan saida Luis Suarez

- Lionel Messi bai ji dadin yadda Luis Suarez ya tashi daga Barcelona ba

- Tauraron Duniyan ya ce ya kamata a karrama ‘Dan wasa irin Suarez

- ‘Dan wasan ya fito ya yi dogon jawabi a Instagram, ya ce za su yi kewa

A Yau ranar 25 ga watan Satumba, 2020, Lionel Messi ya rubuta takardar ban kwana ga Luis Suarez wanda aka sallama daga kungiyar Barcelona.

Wannan wasika mai sosa zuciya ta Lionel Messi ta yi kaca-kaca da shugabannin Barcelona, a dalilin saida Suarez da su ka yi zuwa Atletico Madrid.

‘Dan wasan ya rubuta: “Yau na shiga dakin shiryawarmu sai mummunan lamarin nan ya bujiro mani.” a shafinsa na Instagram ranar Juma’a da safe.

“Ya kamata ace an yi ban-kwana da kai a matsayinka na wanda ka ke; ka na cikin ‘yan wasan da su ka fi kowa muhimmanci a tarihin kungiyar nan.”

KU KARANTA: Suarez: Barcelona ta saida 'Dan wasan da ya ci mata kwallaye 198

Lionel Messi ya yi kaca-kaca da Kungiyar Barcelona a kan saida Luis Suarez
Luis Suarez da sabon Kocin Barcelona Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

“Ba ace an yi waje da kai yadda aka sallame ka ba.” Inji ‘dan wasan Argentina, Lionel Messi.

Tauraron ‘dan wasan ya cigaba da sukar kungiyar kamar yadda ya saba. “Maganar gaskiya ita ce a halin yanzu, babu kuma abin da ya ke bani mamaki.”

Shi ma tsohon ‘dan wasan na kungiyar Liverpool Luis Suarez ya bayyana irin alakarsa da Lionel Messi, ya ce dangantakarsu ba za ta canza ba.

“Zan cigaba da wasa da danyar zimma, da manufar nunawa Duniya cewa zan iya cigaba da gwabzawa."

KU KARANTA: Barcelona ta rabu da manyan ‘Yan wasanta 5 a wata 1

Messi ya ce zai yi masa matukar wahala ya cigaba da wasa babu Suarez. Ya ce: “Za mu yi kewanka sosai. An dade tare, an ci gasa, an ci abinci tare.”

‘Dan wasan ya daura hotunansa tare da Suarez, ya ce ba zai taba mantawa da tarayyarsu ba. “Ina yi maka fatan alheri, ina kaunarka sosai, sai mun hadu abokina.”

Abubuwa ba su tafiya daidai tsakanin shugaban kungiyar Barcelona, Josep Maria Bartomeu da kuma babban ‘dan wasan Duniya, Lionel Messi.

A dalilin haka ne kwanakin baya ‘dan wasan ya rubuta takarda, ya ce zai tashi daga Barcelona.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel