Mace tamkar maza: Matar da ta tsige Shugaba Donald Trump sau biyu a Amurka

Mace tamkar maza: Matar da ta tsige Shugaba Donald Trump sau biyu a Amurka

- Sunan Nancy Pelosi ya zagaye Duniya bayan ta jagoranci tsige Donald Trump

- Nancy Pelosi ce macen farko da ta rike kujerar shugabar majalisa a Amurka

- Pelosi ta kuma kafa tarihin sake karbe kujerarta a 2019 bayan rasa zaben 2011

A ranar 14 ga watan Junairu, 2020, majalisar wakilan kasar Amurka ta tsige shugaban kasa mai shirin barin-gado, Donald Trump daga kan karagar mulki.

Wannan ne karo na biyu da ‘yan majalisar wakilan kasar Amurkan suka tsige shugaba Donald Trump, wanda duk ta jagoranci wannan ita ce Nancy Pelosi.

Mun kawo maku kadan daga cikin tarihin shugabar majalisar Amurka, Madam Nancy Pelosi.

1. A watan Maris ake sa ran Nancy Pelosi za ta cika shekara 81 a Duniya. An haifi ‘yar siyasar ne a shekarar 1940.

2. An haifi Pelosi ne a garin Baltimore, ita ce ‘yar auta kuma macen da iyayenta suka samu a cikin ‘ya ‘ya bakwai.

KU KARANTA: Mata 2 masu tarin dukiya a Afirka

3. Shekaru 57 da suka wuce ta auri Mai gidanta, Paul Pelosi, wani shahararren mai kudi, kuma ‘dan kasuwa.

4. Kafin Pelosi ta shiga siyasa a 1976, ‘danuwanta, Thomas D'Alesandro ya yi siyasa har ya rike ofis tsakanin a 1967.

5. A 1958 wannan Baiwar Allah ta kammala sakandare a wata makarantar coci ta mata zalla da ke yankin Baltimore.

6. Shugabar majalisar ta-yau ta kammala karatun digiri a fannin siyasa a jami’ar Trinity College a Washington a 1962.

7. A shekarar 1987 Pelosi ta bi sahun gidan Philip Burton, ta zama ‘yar majalisa mai wakiltar wani yankin Kalifoniya.

8. Tun shekarar 2003, Nancy Pelosi take jagorantar ‘yan jam’iyyar Democrats a majalisar wakilan kasar Amurka.

KU KARANTA: Abubuwa 10 da ba a sani ba game da macen sojar Najeriya

Mace tamkar maza: Matar da tsige Shugaba Donald Trump sau 2 a Amurka
Nancy Pelosi Hoto: www.nbcnews.com
Source: Twitter

9. Daga baya Pelosi ta kafa tarihi, ta zama shugabar majalisar wakilai, kuma har ta jagoranci tsige shugaban kasar Amurka.

10. Zaben 2020 shi ne na karshe da Pelosi za ta yi a majalisa, wanda ya bata damar rike kujerar shugabar majalisa sau hudu.

A ranar Laraba ne aka tsige Donald Trump daga matsayinsa na shugaban kasar Amurka. Wannan ne karo na biyu da majalisa ta tsige Trump.

A cikin kuri'un da 'yan majalisun suka kada domin tsige shugaban kasar, har da wasu 'yan jam'iyyar Republican dake mulkin Amurka a yanzu.

Yanzu aiki ya ragewa Sanatoci su tabbatar da Donald Trump ya bar ofis, ko su yi watsi da matakin da takwarorinsu a majalisar wakilai suka dauka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel