Abdulmumuni Ningi: Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar Bauchi

Abdulmumuni Ningi: Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar Bauchi

- Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da tsohon dan majalisar dokokin jihar Bauchi, Abdulmumuni Ningi

- An sace Ningi a daren ranar Alhamis, 14 ga watan Janairu kamar yadda rundunar yan sandan jihar ta tabbatar

- Zuwa yanzu dai yan bindigan basu kira don gabatar da bukatunsu ba

Yan bindiga a ranar Alhamis, 14 ga watan Janairu, sun yi garkuwa da tsohon mamba na majalisar dokokin jihar Bauchi, Abdulmumuni Ningi.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, DSP Ahmed Wakili ya tabbatar da sace Ningi ya jaridar Nigerian Tribune a ranar Juma’a, 15 ta watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Gwamnatin tarayya ta bayyana matsayarta kan batun sake rufe kasar

Abdulmumuni Ningi: Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar Bauchi
Abdulmumuni Ningi: Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar Bauchi Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Wakili ya ce:

“Eh, an yi garkuwa da tsohon mamba na majalisar dokokin jihar Bauchi wanda ya wakilci mazabar Ningi a ranar Alhamis, da misalin karfe 8:00 na dare a cikin garin Bauchi”

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa masu garkuwan sun kwace motar Wakili sannan suka yi awon gaba da shi a motarsu.

KU KARANTA KUMA: Mutane sun harzuƙa: Muhimman abubuwa 4 da Garba Shehu ya faɗa game da barazanar MSF ga Kukah

Da yake zantawa da manema labarai, ya kara da cewa:

“...zuwa safiyar nan (Juma’a) da nake magana da ku, basu kira ba tukuna, amma jami’anmu na sirri na aiki don gano tushen lamarin.”

A wani labarin, Yan bindiga sun nemi a biya su naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa kafin sako yaran shugaban tsagin jam'iyyar APC na karamar hukumar Maru da ke Jihar Zamfara, Alhaji Gyare Kadauri Sani, Punch ta ruwaito.

Yaran, Bashar, Abubakar, Haruna, Habibah, Sufyanu, Mubarak da Armiya, an sace su ne a kauyen Kadauri a ranar Juma'a da ta gabata yayin da yan bindiga suka kai hari.

A cewar Gyare, yan bindigan sun kira shi sun fada masa ya samo kudin idan kuma ba haka ba ya manta zancen sake ganin yaransa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel