'Yan bindiga sun sace yaran shugaban APC a Zamfara, sun nemi a basu N50m

'Yan bindiga sun sace yaran shugaban APC a Zamfara, sun nemi a basu N50m

- Yan bindigan da suka sace yaran Alhaji Gyare Kadauri Sani a Zamfara sun nemi a biya su naira miliyan 50

- Sun fada wa shugaban na APC cewa ya manta batun sake ganin yaransa bakwai idan bai biya kudin a kan lokaci ba

- Gyare ya bayyana cewa yana mawuyacin hali don ba shi da kudin kuma ya koka kan yadda hukumomin tsaro ba su tuntube shi ba

'Yan bindiga sun nemi a biya su naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa kafin sako yaran shugaban tsagin jam'iyyar APC na karamar hukumar Maru da ke Jihar Zamfara, Alhaji Gyare Kadauri Sani, Punch ta ruwaito.

Yaran, Bashar, Abubakar, Haruna, Habibah, Sufyanu, Mubarak da Armiya, an sace su ne a kauyen Kadauri a ranar Juma'a da ta gabata yayin da yan bindiga suka kai hari.

A cewar Gyare, yan bindigan sun kira shi sun fada masa ya samo kudin idan kuma ba haka ba ya manta zancen sake ganin yaransa.

'Yan bindiga sun sace yaran shugaban APC a Zamfara, sun nemi a basu N50m
'Yan bindiga sun sace yaran shugaban APC a Zamfara, sun nemi a basu N50m. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan mulkin soja, Ndubisi Kanu, ya rasu

"Sun kira ni sun ce in biya N50m kudin fansar yara na bakwai, sun kuma gargade ni cewa za su kashe yaran idan ban biya kudin a kan lokaci ba," in ji shi.

Da aka tambaye shi ko ya tuntubi hukumomin tsaro da abin ya shafa, Gyare ya ce, "Babu bukatar in gan su tunda sun san abinda ke faruwa da ni kuma babu wanda ya jajanta min."

"Ko sakataren gwamnatin tarayya, Alhaji Bala Bello Maru, da ya fito daga karamar hukumar mu, bai zo gida na ba ko ya min jaje ta wayar tarho."

Ya kuma koka kan yadda shugaban karamar hukumarsa, Alhaji Salisu Dangulbi, shima bai tuntube shi ba game da lamarin.

KU KARANTA: Kukah: FFK ya gargadi ƙungiyar musulmi kan kalamansu

"Ina cikin damuwa matuka; Gani na ke tamkar ni bako ne kuma ban san abinda zan yi ba a yanzu, domin ba ni da kudin da wannan marasa tausayin ke nema," Gyare ya kara.

Ya ce ya fadawa yan bindigan cewa ba zai iya samar da wannan kudin ba ko da ya siyar da dukkan abinda ya mallaka amma dariya kawai suka yi masa.

Gyare ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda hukumomin da abin ya shafa suke nuna halin ko in kula wurin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Kakaki yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu ya ce ya san da batun sace yaran amma bai san an nemi kudin fansa naira miliyan 50 ba.

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairu ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164