Mutane sun harzuƙa: Muhimman abubuwa 4 da Garba Shehu ya faɗa game da barazanar MSF ga Kukah

Mutane sun harzuƙa: Muhimman abubuwa 4 da Garba Shehu ya faɗa game da barazanar MSF ga Kukah

A yayin martani ga barazanar da wata kungiya tayi na neman Bishop Mattew Hassan Kukah ya bayar da hakuri ko ya gaggauta barin jihar Sokoto, fadar shugaban kasa a daren ranar Asabar, 13 ya watan Janairu, ta yi magana tare da kare fitaccen faston.

Kungiyar Musulunci ta Muslim Solidarity Forum (MSF), wacce ke jihar Sokoto, a ranar Talata, 12 ga watan Janairu, ta ce sakon malamin hari ne ga Musulunci kai tsaye sannan ta nemi ya bar jihar.

Da take magana ta hannun mukaddashin shugabanta, Isa Muhammad Maishani, Kungiyar ta kuma bayyana cewa Bishop Kukah na rura wutar rikicin addini ne.

Koda dai malamin da ake magana a kansa ya kalubalanci MSF da ta nuna inda ya caccaki Musulunci ko Musulmai.

Mutane sun harzuƙa: Muhimman abubuwa 4 da Shehu Sani ya faɗa game da barazanar MSF ga Kukah
Mutane sun harzuƙa: Muhimman abubuwa 4 da Shehu Sani ya faɗa game da barazanar MSF ga Kukah Hoto: @NGRPresident @GarShehu
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Benue ta sanya dokar hana fita daga dare zuwa safe, ta bayyana dalili

Amma da yake martani ga barazanar MSF, kakakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya ce Kukah na da yancin yin magana a dokar kasa.

Legit.ng ta jero muhimman abubuwa 4 da Malam Shehu ya ce a martaninsa.

1. A bar Kukah yayi addininsa da siyasa

A cewar hadimin shugaban kasar, kuskure ne yi wa Bishop Kukah barazana saboda baya bisa kundin tsarin mulkin Najeriya.

2. A mutunta yanci da ra’ayin yan Najeriya

Garba Shehu ya ce ya zama dole a mutunta yancin kowani addini tare da bashi damar yin harkokinsa, sannan kuma cewa ya zama dole a mutunta yanci da ra’ayin yan Najeriya.

3. Kukah ya harzuƙa mutane da dama da kalamansa

Koda dai an yi jawabin ne don kare Kukah, fadar Shugaban kasa ta nace cewa lallai furucin malamin na kawo rudani, inda ya harzuƙa mutane da dama da suka dauki abun a matsayin caccakar addinin wasu.

4. Ya zama dole Shugabannin addini da na siyasa su dunga shatawa kansu layi

Shehu ya ce aikin shugabanni ne su dunga kamewa suna shata wa kansu layi wajen fadin maganganu don wanzar da zaman lafiya.

KU KARANTA KUMA: Fitattun Farfesoshi 5 da Coronavirus ta hallaka

A wani labarin, kungiyar CAN ta gargadi wadanda ke yi wa Bishop din Katolika na Sakkwato, Dakta Matthew Kukah, gargadi, da su daina ayyukansu na “haramtacciyar hanya” sannan ta nemi hukumomin tsaro da su tabbatar da tsaron malamin.

Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Sakataren ta, Joseph Daramola, ya bayyana wa manema labarai a ranar Alhamis.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa wata kungiya da ke Sakkwato ta nemi Kukah da ya bar jihar ko kuma gabatar da hakuri game da kalaman da ya yi game da addinin Islama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng