COVID-19: Gwamnatin tarayya ta bayyana matsayarta kan batun sake rufe kasar

COVID-19: Gwamnatin tarayya ta bayyana matsayarta kan batun sake rufe kasar

- Gwamnatin tarayya ta yi martani ga rahotannin cewa tana shirin sake rufe kasar a kan yaduwar COVID-19

- Kakakin gwamnatin ya bayyana matsayar kwamitin COVID-19 kan lamarin

- Wasu yan Najeriya sun rikice kan batun sake komawa dokar kulle

Duk da dawowar annobar COVID-19 a kasar, gwamnatin tarayya ta ce bata tunanin sake rufe kasar.

Kwamitin Shugaban kasa kan korona a ranar Alhamis, 14 ga watan Janairu, ta yi watsi da rahoton cewa tana shirin rufe kasar, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Willie Bassey, kakakin ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya bayyana rahoton sake rufe kasar a matsayin labarin karya.

COVID-19: Gwamnatin tarayya ta bayyana matsayarta kan batun sake rufe kasar
COVID-19: Gwamnatin tarayya ta bayyana matsayarta kan batun sake rufe kasar Hoto: @Chikwe_I
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Mutane sun harzuƙa: Muhimman abubuwa 4 da Garba Shehu ya faɗa game da barazanar MSF ga Kukah

Jawabin ya ce:

“PTF na fatan sanar da cewa babu batun yin haka a kowani taronta ko kuma ba shugaban kasa shawara kan haka.”

Jami’in ya ce irin wannan labarin karyan na iya haddasa fargaba mara ma’ana da tashin hankali a tsakanin mutane.

Ya bukaci yan Najeriya da su yi watsi da rade-radin sannan su ci gaba da bin dokokin COVID-19 da kwamitin ta shimfida.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Benue ta sanya dokar hana fita daga dare zuwa safe, ta bayyana dalili

A wani labarin kuma, jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta yi zargin cewa rashin jajircewa daga bangaren Gwamnatin Tarayya ne ya haifar da karuwar tashin hankali a karo na biyu na annobar Covid-19 da ta addabi kasar, The Nation taruwaito.

Jam'iyyar ta zargi gwamnati da nuna halin ko in kula game da yaduwar annobar ta biyu, lamarin da ta ce, ya haifar da yaduwa da kuma karuwar mutuwa a kasar.

A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, kakakinta, Kola Ologbondiyan, ya koka kan yadda ake samun karuwar mace-macen ‘yan Najeriya cikin har da fitattun‘ yan kasa, a kowace rana daga annobar Covid-19.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel