Junaid Mohammed: Shugaba Buhari ya gaza, karya zai ta yi wa ‘Yan kasa har 2023

Junaid Mohammed: Shugaba Buhari ya gaza, karya zai ta yi wa ‘Yan kasa har 2023

-Junaid Muhammad ya yi martani bayan Shugaban kasa ya fito ya ce tsaro ya karu

-Dattijon ya zargi shugaban kasa Buhari da yabon kansa alhali bai tabuka komai ba

-Tsohon ‘Dan siyasar ya ce babu abin da ya ragewa gwamnati mai-ci sai karyayyaki

Tsohon ‘dan majalisar tarayya a lokacin jamhuriya ta biyu, Dr. Muhammad Junaid, ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta gaza.

A cewarsa shugaba Muhammadu Buhari ya boye gaskiya da ya fito yana cewa an samu saukin matsalar rashin tsaro a Arewa maso gabas da fadin Najeriya.

“Na farko a makon nan, an samu hare-hare uku ko hudu. Kuma duk shugaban da zai ce ya yi kokari maimakon ya ce ya tabuka wani abu, a irin wannan yanayi, ba gaskiya ya nufa ba.”

Kara karanta wannan

Dalilin Na Yasa Muka Nemi Afuwar Yan Najeriya Kan Yadda Muka Gudanar Da Mulki, Aisha Buhari

“Babu mai sha’awar tashin hankali da rashin tsaro, amma ba daidai ba ne shugabanni su kirkiri karya saboda su yabi kansu a kan abin da ba su yi ba.” Inji Dattijon.

KU KARANTA: Tsaro: An samu ci gaba sosai a Borno, Yobe da Adamawa - Buhari

Junaid Mohammed ya ce mai girma shugaban kasa bai taimakawa gwamnatinsa, jam’iyyarsu da jami’an tsaro da wannan magana da ya yi ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dr. Mohammed ya ari kalaman tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln, wanda ya ce da zarar al’umma sun daina yarda da shugabansu, to shikenan.

Ya ce: “Za ka iya yaudarar wasu mutane a wasu lokuta, amma ba za ka yaudari kowa a kowane lokaci ba, ba za ka yi nasara da yaudarar jama’a a ko da yaushe ba.”

A cewar dattijon babu abin da gwamnatin Muhammadu Buhari za ta iya, sai dai ta yi ta karya har 2023.

Kara karanta wannan

Saura Wata 7 a Bar Ofis, Buhari Ya Fadawa Ministoci Su Fara Shirye-Shiryen Mika Mulki

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun ceto mutane 800 da aka yi garkuwa da su a 2020 - Buhari

Junaid Mohammed: Shugaba Buhari ya gaza, karya zai ta yi wa ‘Yan kasa har 2023
Junaid Mohammed da Shugaba Buhari Hoto: www.dmo.gov.ng da www.vanguardngr.com/2021/01/insecurity-buhari-has-failed-woefully-%E2%80%95-junaid
Asali: UGC

“Sun gaza war-was, ‘Yan Najeriya har da tsofaffin shugaban kasa sun fito sun ce Najeriya ta lalace. Ban ga ta yadda shugaba zai fara fitowa yana yabon kansa ba.”

Dazu kun ji cewa Hedikwatar tsaro tace Operation Delta Safe ta samu nasarar damke wasu mutane 2 a hanyar ruwan Effiat a Akwa-Ibom da ke fasa-kauri.

Sanarwar ta ce ana zarginsu da laifin sumogal da buhuna 1,184 na takin zamai a makon da ya wuce.

Kakakin rundunar sojin kasa, Jaar John Enenche ya sanar da manema labarai wannan a Abuja, yace 'yan ta'adda suna amfani da takin wurin hada bam mai tashi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng