Femi Adesina yace a 2020, sojoji sun kashe Miyagu da Boko Haram 2, 403 tsakanin Maris-Disamba
-Sojojin Najeriya sun hallaka ‘Yan ta’adda fiye da 2, 400 a shekarar da ta wuce
-Tsakanin Maris zuwa Disamba, an ceto mutane 800 da aka yi garkuwa da su
-Femi Adesina ya ce a daidai wannan lokaci an kama marasa gaskiya har 1900
A jiya Alhamis, 14 ga watan Junairu, 2020, fadar shugaban kasa ta fito ta bayyana nasarar da dakarun sojojin Najeriya suka samu a kan ‘yan ta’adda.
Jaridar Daily Trust ta rahoto Femi Adesina ya na cewa jami’an tsaro sun hallaka tsageru, ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane 2, 403.
Mai magana da yawun bakin shugaban kasar yace sojojin sun yi wannan namijin aiki ne tsakanin ranar 18 ga watan Maris zuwa 30 ga watan Disamban 2020.
Femi Adesina ya bayyana wannan ne a jerin nasarorin da dakarun sojojin suka samu a ranar da ake tunawa da bautar da jami’an tsaro su ka yi wa Najeriya.
KU KARANTA: Sojoji, ‘Yan Sanda da KASTELEA sun dura gidan Dahiru Bauchi da tsakar dare
Kamar yadda hadimin na Muhammadu Buhari ya bayyana, bayan haka an samu nasarar hallaka ‘yan ta’adda da-dama a harin da jiragen yaki su ke kai wa.
Nasarorin da fadar shugaban kasar ta zayyana sun nuna a halin yanzu, an samu saukin ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
“Bayan nan an ceto mutane 864 da aka yi garkuwa da su a Najeriya, Sannan an karbo litoci 9,684,797 na fetur da litoci 33,516,000 na kananzir da aka sace.”
Femi Adesina ya kara da cewa: “Bugu da kari, marasa gaskiya 1, 910 aka kama, sannan an samu miyagun makamai da harsashai a hannunsu a wannan lokaci.”
KU KARANTA: Masu kiran mutane suna muryar aljanu sun shiga hannun ‘Yan Sanda
Har ila yau, dakarun sojojin sun gano ganga 46,581.8 na danyen mai da litocin kananzir 22,881,257 da aka sace, sannan dakarun OSR sun karbe kayan N12.5bn.
A jiya kun ji cewa rundunar Sojojin kasa tana cigaba da samun galaba a kan ‘Yan ta'addan Boko Haram da su ka hana mutanen Arewa maso gabas sakat.
Dakarun Sojojin Najeriya sun ce ragargaji ‘Yan ta’addan Boko Haram fiye da 60 a jihar Yobe.
A wata sanarwa, hedikwatar jami’an tsaro ta kasa ta ce ‘yan ta’adda 64 ta kashe a jihar Yobe a cikin mako guda a ba-ta-kashin da su kayi da dakarun sojoji.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng