Dakarun soji sun kwace taki mai yawa da aka yi sumogal din shi, DHQ
- Hedkwatar tsaro ta ce Operation Delta Safe ta samu nasarar damkar wasu mutane 2 a hanyar ruwan Effiat dake karamar hukumar Mbo a Akwa-Ibom
- Ana zarginsu da yin sumogal din buhunhuna 1,184 na takin Yaraliva Nitrabor, a ranar 9 ga watan Janairun 2021 ta kasar Kamaru
- Kakakin rundunar soji, John Enenche ya sanar da manema labarai a Abuja, inda yace 'yan ta'adda suna amfani da taki wurin hada abubuwa masu fashewa
Hedkwatar tsaro ta ce rundunar Operation Delta Safe, a ranar 9 ga watan Janairu, sun kwace buhunhuna 1,184 na Yaraliva Nitrabor Fertilizer wuraren hanyar ruwan Effiat dake karamar hukumar Mbo dake jihar Akwa Ibom.
Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai akan sojoji, inda yace tsakanin 7 ga watan Janairun 2020 zuwa 13 ga watan Janairun lamarin ya faru, a ranar Alhamis a Abuja.
Enenche ya ce suna zargin an yi sumogal din takin ne ta wani katon jirgin ruwa na katako ta kasar Kamaru.
KU KARANTA: Masoyan da suka adana N4.5m tsawon shekaru 5 sun hada shagalin bikinsu mai kayatarwa da kudin
A cewarsa, wadanda ake zargin sun yi sumogal yanzu haka suna hannun Operation Delta Safe kuma za a mika su hannnun hukuma don daukar mataki akansu.
Enenche ya ce ONSA ta sanya doka akan hana shigo da taki daga kasashen ketare da siyar dasu.
"Duk da ana amfani da taki akan harkar noma, amma 'yan ta'adda da sojoji su na amfani dashi wurin hada abubuwa masu fashewa saboda sinadarin ammonium nitrate din da yake cikinsa.
"Sannan shigowa da taki zai iya kawo cikas ga tsaron kasar nan, musamman halin da kasar nan ta tsinci kanta," a cewarsa.
KU KARANTA: Bidiyon Dino Melaye yana kwasar rawar wakar kungiyar maza marowata
A wani labari na daban, rundunar Operation Lafiya Dole a ranar Talata ta ragargaza mayakan ta'addanci na Boko Haram kuma sun lalata motcoin yakin 'yan ta'addan a wani samame da suka kai ta jiragen yaki a Mainok da ke Borno, hedkwatar tsaro tace.
Shugaban fannin yada labarai an tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, Daily Trust ta wallafa.
Enenche ya ce an kai harin ne bayan bayanan sirri da aka samu wanda ya nuna cewa 'yan bindigan na kai kawo a Jakana-Mainok na jihar da motocin yaki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng