Kallabi tsakanin rawuna: Mata 2 masu tarin dukiya a Afirka

Kallabi tsakanin rawuna: Mata 2 masu tarin dukiya a Afirka

Arziki dai ubangiji ne ke badawa. Yana ba wanda yaso kuma a lokacin da yaso. Ana neman azrziki ne ta hanyar neman shi don baya zuwa inda mutum ke kwance. Duk idan kaji wane, toh ba haka kawai bane. Ya tashi ya nema da iyakacin iyawarsa.

Folorunso Alakija ta kasar Najeriya da kuma Isabel dos Santos ta kasar Angola su ne matan da suka fi kowacce mace kudi a nahiyar Afirka.

Suna da jimillar arzikin da ya kai dala biliyan 3.2, kamar yadda Forbes ta bayyana

Babbar ‘yar kasuwar man fetur ta Najeriya, Folorunso Alakija da kuma Isabel dos Santos ta kasar Angola ne suka bayyana a matsayin mata biyu da suka fi kowacce mace kudi a nahiyar Afirka kamar yadda Forbes ta kiyasta.

1. Isabel dos Santos

Babbar ‘yar kasuwa ce da ta tara arzikinta ta ne ta hanyar saka hannayen jari. Matar ‘yar kasar Angola mai shekaru 43 na da kimanin dala biliyan 2.2. Ita ce babbar diyar tsohon shugaban kasar Angola, Jose Eduardo.

Kallabi tsakanin rawuna: Mata 2 masu tarin dukiya a Afirka
Kallabi tsakanin rawuna: Mata 2 masu tarin dukiya a Afirka
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyon tsiraicin wani Sanata: Kowa nayi, wasu sun fi wasu wayau - Sanata mai jaje

2. Folorunso Alakija

Folorunso Alakija na da shekaru 68 a duniya kuma tana daya daga cikin mata bakake da suka fi kudi a nahiyar Afirka. Attajirar ta tara wannan dukiyar ne ta hanyar kasuwancin man fetur.

Mamallakiyar kamfanin Famfa din ta kware ne a fitar da man fetur daga kasar nan ta karkashin kamfaninta mai suna Famfa oil Limited. Jimillar azrkinta ya ka dala biliyan 1.

Kallabi tsakanin rawuna: Mata 2 masu tarin dukiya a Afirka
Kallabi tsakanin rawuna: Mata 2 masu tarin dukiya a Afirka
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng