Kallabi tsakanin rawuna: Abubuwa 10 da ba a sani ba game da Arotile

Kallabi tsakanin rawuna: Abubuwa 10 da ba a sani ba game da Arotile

Kallabi tsakanin rawuna, mace ta farko da ta zama matukiyar jirgin yaki a rundunar sojin saman Najeriya, Tolulupe Arotile, ta rasu sakamakon hatsarin mota a Kaduna.

Rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da rasuwar Arotile a ranar Talata, sakamakon raunikan da ta samu daga hatsarin mota.

Baya ga zamanta mace ta farko matukiyar jirgin sama na yaki, akwai abubuwa da yawa ta yuwu ba a sani ba game da matukiyar jirgin saman. Ga kadan daga ciki:

1. Tolulope Arotile 'yar asalin yankin Iffe ce da ke karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi kuma an haifeta a shekarar 1995.

2. Arotile ta halarci makarantar firamare da sakandaire ta sojan sama da ke Kaduna.

3. Ta shiga makarantar koyon tukin jirgin sama ta dakarun sojin saman Najeriya a ranar 22 ga watan Disamban 2012.

4. A 2017, ta kammala karatunta a makarantar koyon tukin jirgin sama da ke Kaduna kuma ta zama sojan sama a ranar 16 ga watan Satumban 2017.

Kallabi tsakanin rawuna: Abubuwa 10 da ba a sani ba game da Arotile
Kallabi tsakanin rawuna: Abubuwa 10 da ba a sani ba game da Arotile. Hoto daga Defence HQ
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An bi mamallakin kamfani GoKada an kashe har gida

5. An zabeta don zuwa horarwa a kasar Afrika ta Kudu bayan hazakar da ta nuna yayin karatunta a makarantar koyon tukin jirgi da ke Kaduna.

6. A ranar 15 ga watan Oktoban 2019, ta samu sa'o'i 460 na tukin jirgin sama a cikin watanni 14.

7. An karrama Arotile a matsayin mace ta farko da ta zama matukiyar jirgin yaki a rundunar sojin saman Najeriya a cikin shekaru 55 da rundunar tayi da samuwa.

8. Ministar harkokin mata da ci gaba, Dame Pauline Tallen da shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar sun karramata a watan Oktoba 2019.

9. Ba a kai shekara daya ba da karramata, Arotile, wacce ita ce macen farko a Najeriya da ta zama matukiyar jirgin yaki, ta rasu sakamakon hatsarin mota tana da shekaru 24 a duniya.

10. A yayin rayuwarta takaitacciya amma mai cike da amfani, marigayiya Arotile ta taka rawar gani wurin ganin bayan 'yan bindiga da suka addabi jihohin arewa ta tsakiya. Tana tuka jirgin yakin Operation Gama Aiki a Minna, jihar Neja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel