Katsina: ‘Yan Sanda sun kama masu fakewa da sunan Aljanu suna damfarar jama’a

Katsina: ‘Yan Sanda sun kama masu fakewa da sunan Aljanu suna damfarar jama’a

- Dakarun ‘Yan Sanda sun cafke wasu masu cutar jama’a da sunan Aljanu a Katsina

- Wadannan mutane suna kiran mutane a wayar salula, suna yi masu muryar Aljanu

- Dubunsu ta cika lokacin da su ka nemi su damfari wata Baiwar Allah a garin Mani

Dakarun ‘yan sanda a jihar Katsina sun gabatar da wasu mutane biyu da ake zargi da laifin damfara; Kabiru Bashir da Sadiq Ashiru.

Daily Trust ta bayyana cewa Kabiru Bashir mai shekara 27 da Sadiq Ashiru 'dan shekara 30 duk mutanen karamar hukumar Danbatta ne a jihar Kano.

Jaridar ta rahoto cewa wadannan mutane sun kware wajen yaudarar Bayin Allah, suna kiransu a wayar salula, suna yi masu karyar su aljanu ne.

Da ake gabatar da wadanda ake zargin, kakakin ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ya ce an yi ram da su ne suna shirin damfarar wata mata.

KU KARANTA: 'Yan sandan jihar Bauchi sun kama wani matashi da laifin shirya badala

An gabatar da wadannan mutane biyu gaban ‘yan jarida a ranar Laraba, 8 ga watan Junairu, 2021 da kimanin karfe 12:00 na rana a babban ofishin ‘yan sanda.

Mai magana da yawun bakin ‘yan sanda na Katsina, Isah ya ce wadanda ake zargi sun sacewa wata mata mai suna Rabia Garba katin ATM a garin Mani.

“Daga nan sai su ka kira ta a wayar salula, suna cewa su aljanu ne, su ka bukaci ta ba su lambar sirrinta.” Inji SP Gambo Isah.

“Wadanda ake zargi sun nemi su yaudare ta, suka fada mata suna shirin aiko mata Naira miliyan daya a asusunta, suka ba ta umarni ta je bankinta a Katsina.”

KU KARANTA: Amaryar gwamnan jihar Nasarawa ta haifi tagwaye

Katsina: ‘Yan Sanda sun kama masu fakewa da sunan Aljanu suna damfarar jama’a
Kabiru Bashir da Sadiq Ashiru Hoto: www.lindaikejisblog.com
Asali: Twitter

A nan ne wannan mata ta fara zargin akwai wani abu, sai ta kai kara wajen ‘yan sanda. Wadanda aka kama sun fadi irin ta’adin da suka yi wa jama’a.

Idan za ku iya tunawa, mun samun labarin jami’an tsaro sun cafke mutumin da yace zai biya kudi a kashe shugaban kasa Muhammadu Buhari da Abba Kyari

Wannan Matashi ya tabo tsuliyar dodo bayan ya ce zai sa a bindige Buhari da tsohon Hadiminsa a Twitter.

'Yan sandan sun jero kayan satar da aka samu wajen wadannan mutane, su ka ce za a kai su kotu nan gaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng