Liyafar badala: 'Yan sanda sun damke samarin da ake da shiryawa a Bauchi
- 'Yan sandan jihar Bauchi sun damki wasu matasa a karamar hukumar Dass, wadanda ake zargin suna shirin yin liyafar lalata da holewa
- Al'amarin ya faru ne a ranar Laraba, bayan bayyanar labarin fara shirye-shiryen yin liyafar, kuma dama sun dade suna addabar jama'a da sace-sace
- Cikin matasan da aka kama duk masu karancin shekaru ne, har da wani Sara-Suka mai shekaru 19, inda aka kwace makamai da dama a hannunsu
'Yan sandan jihar Bauchi sun kama wani matashi mai shekaru 19, wanda aka fi sani da Sara-Suka, bisa laifin shirya liyafar lalata da holewa a karamar hukumar Dass dake jihar.
Yayin da 'yan sandan hedkwatar Yan doka dake babban birnin jihar suka fita sintiri a ranar Laraba, kwamishinan 'yan sandan, CP Lawan Tanko Jimeta ya ce wadanda ake zargin sun addabi al'umma da hatsabibanci da kwacen wayoyi.
Ba anan kadai suka tsaya ba, ana zarginsu da shirya wata liyafa, wacce ake zargin ta holewa da lalata ce a garin Dass a ranar 11 ga watan Janairu, The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai hari kauyen Kaduna, sun halaka mutum 2
CP din, wanda ya samu wakilcin kakakinsa, Ahmed Wakili, ya ce kwamandan RRS ne ya jagoranci wani sintirin da aka kama samarin.
Ya bayyana sunayensu, inda yace akwai Ishaya Adamu mai shekaru 19, Mohammed Abdullahi Lawwali, mai shekaru 22, Ayuba Adamu mai shekaru 19, Aminu Tago 19, Anas Sulaiman alias (Danarna) 16, Yusuf Ahmed 20 da Abba Abdullahi mai shekaru 20.
Sauran sun hada da Sulaiman Umar, 20,, Abdulrashid Ali 17, Aliyu Iliya 15, Idris Sulaiman 22, Nuru Sarki 17, Ibrahim Musa 29, Musa Danasabe 17, Abdulrashid Anas 18, Ibrahim 22 da Kasimu Haladu mai shekaru 26, duk a garin Dass a jihar Bauchi.
KU KARANTA: Mashahurin mai kudin duniya, Elon Musk, ya tafka asarar $14 biliyan a rana daya
Bincike ya nuna cewa an kama su ne cikin kankanin lokaci, bayan sun fara shirye-shiryen hada liyafar ta holewa yasu-yasu.
An kwace abubuwa daga hannayensu da suka hada da Ranki daya, tsitaka daya, adduna da wukake. Yanzu haka an tura su kotu don daukar mataki akansu.
A wani labari na daban, wani mutumi daga yankin arewa maso gabas na kasar nan ya kalubalanci yadda ake tsawwala al'amuran aure a kasar Ibo.
A yayin da ya yi dogaro da wani lissafi tare da jerin kayan da ake bukata ango ya kaiwa dangin amarya a Nnewi na jihar Anambra, mutumin ya yi korafin ta shafinsa na Twitter.
Ya ce matasa a kasar Ibo suna shan wahala. Ya dace a rage yawan abubuwan da ake bukatar matashi ya kai idan yana neman aure.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng