Abin da Emmanuel Akuma ya fada a shafin Twitter ya jawo FCID sun yi ram da shi

Abin da Emmanuel Akuma ya fada a shafin Twitter ya jawo FCID sun yi ram da shi

- Emmanuel Akuma ya fito Twitter ya na cewa zai sa a bindige Buhari da Abba Kyari

- Jami’an ‘Yan Sanda sun cafke Akuma saboda wannan barambarama da ya yi a 2017

- Mahaifin wannan matashi ya ce tun Afrilun 2020, ‘yan sanda ke tsare da yaron na sa

Solomon Akuma mahaifin wani matashi da ke aiki da hukumar NAFDAC, Emmanuel Akuma, ya bada labarin yadda ‘dan sa ya shiga hannun ‘yan sanda.

Jaridar Premium Times ta ce Solomon Akuma wanda Fasto ne a cocin Truevine Evangelical Mission da ke Delta, ya ce dakarun FCID sun cafke masa yaro.

Solomon Akuma ya shaidawa jaridar cewa tun watan Afrilun 2020, ‘yan sanda suka kama Emmanuel Akuma mai shekaru 29 a garin Aba, jihar Abia.

Wannan matashi ya zo shafin Twitter yana cewa zai biya ‘yan bindigan kasar Rasha kudi domin su harbe shugaban kasa (Buhari) da Marigayi Abba Kyari.

KU KARANTA: Abubuwa 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari

Akuma ya yi wannan ganganci ne bayan wani ya jefa tambaya a shafin twitter, ya na tambayar mutane abin da za su yi idan suka samu daka miliyan $1m.

Mahaifin wannan yaro ya ce: “Da ni su ka yi amfani suka kama yarona. Sun bincika sun gano ni fasto ne.” A haka ‘yan sanda su kayi masa tarko, suka kama shi.

“Wani ya kira ni ya fada mani cewa na taba yi masa addu’a, ya ce yana so ya karrama ni tare da wasu, ya fada mani lokacin da zai zo.” Sai ga Akuma a hannun FCID.

Daga nan kami’an tsaron su ka yi nasarar cafke matashin, su ka tsare shi a Abuja. Bayan wata uku aka gurfanar da shi a kotu bisa zargin aikata wasu tarin laifuffuka.

KU KARANTA: Fitattun mutanen da ake yi wa hangen kujerar Kyari

Abin da Emmanuel Akuma ya fada a shafin Twitter ya jawo FCID sun yi ram da shi
Pharm. Emmanuel Akuma Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Tun 2017 Akuma ya yi wannan barambarama, amma yanzu watanni tara kenan ana cigaba da tsare shi. Marigayi Abba Kyari ya rasu a lokacin ya na tsare.

Idan za ku tuna, daga baya hadimin shugaban kasa, Abba Kyari ya rasu a sakamakon annobar COVID-19 a garin Legas.

Twitter ya na amayar da gawurtattun Masoyan Trump da ke tada zaune tsaye a kasar Amurka.

Kamfanin Twitter ya fito ya bayyana abin da ya sa ya ke fatattakar ‘yan a-mutun Shugaba Donald Trump daga amfani da shafin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng