Donald Trump ya yi martani bayan tsige shi

Donald Trump ya yi martani bayan tsige shi

- A daren ranar Laraba ne majalisar kasar Amurka ta saka kuri'ar tsige Shugaban kasa DonaldTrump

- Hakan ya biyo bayan zarginsa da majalisar tayi da amfani da kujerarsa wajen tirsasa wata kasa yakar kishiyarsa na siyasa

- Duk da dai Donald Trump ya musanta hakan, ya ce tun farko dama suna neman hanyar tsigesa

A daren Laraba ne majalisar wakilan kasar Amurka suka saka kuri’ar tsige Shugaban kasa Donald Trump, a kan hanasu bincike da kuma amfani da karfin kujerarsa ba ta yadda ya dace ba, wajen mu’amala da kasar Ukraine.

Za a mika sakamakon ga majalisar dattawan kasa, inda za a yanke hukuncin karshe a kan tsige shugaban kasar Amurka din daga kujerarsa a wata mai zuwa.

A yayin mayar da martani game da tsigesa a shafinsa na tuwita, Donald Trump ya wallafa hotonsa dauke da rubutu kamar haka: ‘A sahihance, ba ta ni suke ba, ta ku suke yi, ni ne dai a kan hanyar.’

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Majalisa ta tsige shugaban kasar Amurka

Trump ya musanta duk laifukan da ake zarginsa dasu, ya shiga cikin zanga-zangar Michigan a lokacin da suke kada kuri’ar tsigesa. Ya ce: “Suna ta kokarin tsigeni tun daga ranar farko da na hau mulki.”

Bayan shekaru uku da kokarinsu na neman laifina, a daren yau majalisar wakilai na kokarin shafe wahala da kuri’un mutane miliyan 10 masu kishin kasar Amurka.” cewar Trump.

A halin yanzu, Donald Trump ne shugaban kasar Amurka na uku a tarihi da aka tsige, bayan Andrew Johnson da Bill Clinton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel