Na koma APC ne domin na gina rayuwar ‘ya’yana, In ji Sanata Abbo

Na koma APC ne domin na gina rayuwar ‘ya’yana, In ji Sanata Abbo

- Har yanzu Sanata Ishaku na cike da farin ciki kan sauya shekar da yayi kwanaki zuwa APC

- A yanzu sanatan ya bayar da dalilansa na yanke gagarumin hukuncin sauya shekar a shekarar da ta gabata

- Sanata Abbo ya kuma nuna karfin gwiwar cewa APC za ta karbe jihar Adamawa a 2023

Sanata Elisha Ishaku Abbo ya bayar da Karin dalilan da ya sa shi sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga Peoples Democratic Party (PDP).

Abbo wanda yayi magana a wani taron masu ruwwa da tsaki a sakatariyarta da ke Yola, babbar birnin jihaar Adamawa, ya ce ya koma jam’iyyar ne domin ginawa yaransa da jihar maakomar rayuwa mai kyau.

Legit.ng ta tattaro cewa taron ya samu halartan manyan yan siyasa a jihar wadanda suka sauya sheka zuwa APC kwanaki tare da Sanata Abbo.

Na koma APC ne domin na gina rayuwar ‘ya’yana, In ji Sanata Abbo
Na koma APC ne domin na gina rayuwar ‘ya’yana, In ji Sanata Abbo Hoto: Senator Ishaku Abbo
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Fadar Shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari bai kawo karshen rashin tsaro ba

Sun hada da tsohon gwamna, Bala James Ngilari da tsohon dan takarar gwamna, Sanata Abdulaziz Nyako.

A wani jawabi daga ofishin Sanata Abbo wanda Legit.ng ta nado yana cewa:

“Na koma APC ne domin na ginawa ‘ya’yana jihar Adamawa mai kyau; ba wai don mulki ba. APC da muke ciki, kawai yan Najeriya da jihar Adamawa ne a zuciyarmu.

“Mu ba mayun siyasa bane; mu ba yan siyasan a mutu ko ayi rai bane da burinsu hawa kujerar mulki. Mun hada kaine domin mu ceto jihar Adamawa dagfa wadannan barayin mutane da ke mulki.

“Mun damu da ra’ayin jihar Adamawa, bama maitar son mulki.”

Sanatan wanda ke wakiltan yankin Adamawa ta arewa ya zargi Gwamna Ahmadu Umaru Fintiro da boyewa a karkashin inuwar aikin da Bankin duniya da majalisar dinkin duniya da kungiyoyin kasa da kasa ke yi tun bayan da ya karbi mulki.

KU KARANTA KUMA: Rikicin PDP ya munana yayinda kwamishinan Ikpeazu ya caccaki gwamnan da wasu bayan ya karbi bakuncin Orji Kalu

A cewarsa, gwamnan bai da aiki ko daya da zai nuna da sunan nasa duk da dukiyoyi da basussukan da gwamnatinsa ta ciyo.

Sanata Abbo ya bayyana cewa hadin kai ne kadai zai kai APC mataki na gaba, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su yi aiki tare don cimma nasararsu a 2023.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Adamawa, Ahmed Umaru Fintiri, ya nuna juyayi tare da bayyana alhinin rasuwar jigo a jam'iyyar PDP, Alhaji Ahmed Song.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa marigayi Ahmed ya rasu ranar Talata, 12 ga watan Janairu, 2021, yana da shekaru 75 a duniya.

A sakonsa na ta'aziyya, gwamna Fintiri ya bayyana cewa rasuwar Alhaji Ahmed babban rashi ne da ya girgiza shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel