Fadar Shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari bai kawo karshen rashin tsaro ba
- Fadar shugaban kasa ta yi martani kan matsalolin tsaro a Najeriya
- Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana abunda Buhari ke yi don magance matsalolin tsaro
- Shehu yana da yakinin cewa gwamnati mai ci za ta yi nasara a kokarinta na tsaron kasar
Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke fuskantar kalubale wajen kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.
Garba Shehu, kakakin shugaban kasa ya ce matsalolin tsaro a kasar na rikedewa, saboda haka yake kara tabarbarewa.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Shehu ya bayyana hakan ne a yayinda ya bayyana a shirin Television Continental (TVC) a ranar Lahadi, 10 ga watan Janairu.
KU KARANTA KUMA: Dokta Bashir: Idan mutum ya saki matarsa a shirin fim to ya saki matarsa ta gida ne
Sai dai ya ba yan Najeriya tabbacin cewa shugaban kasar na aiki tukuru don tsare kasar.
Ya ce:
“Kasar nan na fama da matsalolin rashin tsaro a koda yaushe. Babu kasar da bata fama da laifuka. Matsalolin na rikidewa... amma duk ana iya bakin kokari a yanzu.”
Shehu ya ce Buhari ya jajirce don magance Boko Haram, fashi da makami da sace-sacen mutane a 2021.
KU KARANTA KUMA: Rikicin PDP ya munana yayinda kwamishinan Ikpeazu ya caccaki gwamnan da wasu bayan ya karbi bakuncin Orji Kalu
A wani labarin kuma, Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yada labarai, ya ce shugaban kasa bai sallami shugabannin tsaro ba ne saboda yana hango wata nagartarsu da 'yan Najeriya basu gani.
Shehu ya sanar da hakan a wani bakuncinsa da TVC ta karba kuma jaridar Vanguard ta ruwaito.
A yayin martani ga tambayar da aka yi masa a kan abinda ya hana Buhari ya sallami shugabannin tsaro duk da yadda ake ta bukatar yayi hakan, Garba ya ce:
"Saboda yana ganin abinda masu caccaka basu gani. Yana ganin abinda mutane da yawa basu gani. Ba nadi bane mai wa'adi. Babu wata doka da tace sai shugabannin tsaro an sallamesu bayan sun kwashe shekaru biyu.
"Suna aiki ne da gamsuwar shugaban kasa. A yanzu kuwa shugaban kasan ya ce zai yi gyaran. Toh ya rage gare shi ne kawai. Ina tunanin ya dace 'yan Najeriya su bada uziri."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng